Yadda hatsarin jiragen ruwa ya ci rayuka 108 a Sakkwato
[ad_1]
Hatsarin jiragen ruwa ya ci rayuka akalla 108 a Jihar Sakkwato a cikin shekaru biyar da suka gabata.
Mutane da dama sun bace a sakamakon hatsarin jiragen ruwan da aka samu akalla sau takwas a jihar a daga shekarar 2020 zuwa yanzu.
Bincikenmu ya gano cewa daga shekarar 2020 zuwa 2025 an rasa rayuka akalla 1,600 a sanadiyyar hatsarin jiragen ruwa a sassa daban na Najeriya.
Na baya-bayan nan shi ne wanda ya auku a ranar Lahadi, inda jirgin ruwa dauke da fasinjoji 51, inda aka yi nasarar ceto mutum 26, wasu 25 ake ci gaba da neman su a yankin Karamar Hukumar Goronyo da ke Jihar Sakkwato.
Nigeria na da albarkatu masu yawa, ciki har da hanyoyin ruwa da ke yawo a jihohi 28, suna da tsawon fiye da kilomita 10,000. Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Kasa (NIWA) ta bayyana cewa kimanin kilomita 3,800 daga cikin wadannan hanyoyin ruwa ana safara da su wajen safarar kaya da fasinjoji.
Sai dai duk da wadannan albarkatu, Najeriya na ci gaba da fuskantar asarar rayuka a hanyoyin ruwa sakamakon rashin tsauraran dokoki da kuma rashin bin ka’idojin tsaro.
Binciken Hukumar Binciken Hadurra ta Najeriya (NSIB) ya nuna cewa fiye da rabin mutanen da suka mutu a hadurran jirgin ruwa sun mutu ne ta hanyar nutsewa, kashi 90% daga cikinsu ba su sanya rigar kare rai ba .
A Arewacin Najeriya, inda ake ci gaba da amfani da kwalekwalen gargajiya a matsayin hanyar sufuri, daruruwan mutane sun rasa rayukansu a cikin shekaru.
Hatsarin jiragen ruwan Sakkwato a shekara 5
A Jihar an samu hadurran jirgin ruwa guda tara tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 108:
Agusta 2020 – Birjingo, Goronyo
Mutane 9, yawancinsu mata da yara, sun mutu bayan jirgin ruwa ya kife da su a hanyarsu ta zuwa aikatau a gonar shinkafa a yankin Birjingo da ke Karamar Hukumar Goronyo. Masunta sun ceto wasu daga cikin fasinjojin kwalekwalen da yake dauke da fasinjoji fiye da kima.
Yuni 2021 – Shagari
Mutane goma sha uku sun mutu, ciki har da matan aure da yara da tsofaffi, a hadarin jirgin ruwa tsakanin Doruwa da Ginga da ke Karamar Hukumar Shagari. An danganta hatsarin da daukar kaya da mutane fiye da kima.
Afrilu 2022 – Gidan Magana, Shagari
Mutane 29, akasarinsu yara ’yan shekaru 9 zuwa 17 ciki har da wata amarya da ake shirin daura aurenta, sun mutu yayin da suke ketare kogin don samo itacen girki a yankin Gidan Magana da ke Karamar Hukumar Shagari. Cikin mamatan har da yara biiyar ’yan gida daya. Fasinjoji shida ne kawai suka tsira. Direban jirgin ya tsere.
Mayu 2023 – Dandeji, Shagari
Aƙalla ’yan mata 15 sun mutu bayan jirgin ruwa dauke da fasinjoji 40 ya kife a yankin Dandeji, Karamar Hukumar Shagari, inda masunta suka gano gawawwaki 15, aka ci gaba da neman sauran.
Agusta 2024 – Dundaye, Wamakko
Mutane hudu sun mutu, daya ya bace bayan jirgin ruwa da ke dauke da manoma ya kife a yankin Dundaye da ke Karamar Hukumar Mamakko. Hukumar NEMA da sauran hukumomi sun jagoranci aikin ceto.
Disamba 2024 – Tangwale, Dundaye
Mutum ɗaya mai shekaru 60 ya mutu a hadarin jirgin ruwa da ke dauke da fasinjoji 35. An ceto mutane 34, an binne mamacin bisa tsarin Musulunci bayan aukuwar hatsarin a yankin Tangwale da ke yankin Dundaye.
Yuni 2025 – Rinaye, Shagari
Mutane bakwai sun mutu bayan kifewar kwalekwale a yankin Rinaye, a hanyar Gidan Husaini zuwa Gwargawu a Karamar Hukumar Shagari. Wadanda suka mutu sun hada da yara biyu da matan aure uku.
Agusta 2025 – Kojiyo, Goronyo
Aƙalla ’yan kasuwa 30 sun mutu bayan jirgin ruwa da ke dauke da fasinjoji 51 da kaya ya kife a ranar Lahadi, 17 ga Agusta, a yankin Kojiyo, a kan hanyar zuwa kasuwar Goronyo. An ceto fasinjoji 25, wasu 26 sun bace.
Martanin Gwamnatin Sakkwato
A shekarar 2024, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sayi jiragen ruwa masu injin, rigunan kariya da kayan agaji da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.1 don raba wa kananan hukumomi 22 da ke fama da ambaliya.
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Ibrahim Dade Adare, ya ce rabon ya biyo bayan rahoton kwamitin da ya tantance yankunan da ambaliya ke shafa.
Bayan hadarin Agusta 2024, Gwamna Ahmed Aliyu ya bayar da tallafin Naira miliyan 30 ga iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka tsira. Iyalan kowane mamaci sun samu Naira miliyan 5, wadanda suka tsira kuma sun samu Naira 500,000.
Gwamnan ya yi kira da a guji sakacin da ke haddasa hadurra. Ya ce, “An shaida min cewa wasu fasinjoji sun yi sakaci da ya janyo hadarin. Koginmu albarka ne, amma dole ne mu fifita tsaro.”
Matsalar ta shafi kasa
Alkaluman Hukumar HYPPADEC, mai kula da yankunan da ke samar da wutar lantarki, sun nuna cewa hatsarin jiragen ruwa sun lakume rayuka akalla 350 a shekarar 2020 kadai a sassan Najeriya.
Shugaban HYPPADEC, Hon. Joseph Terfa Ityav, ya danganta hadurran da lalacewar jiragen ruwa, cika da kaya, rashin rigar kariya da kuma itatuwan da ke cikin ruwa.
Bincikenmu ya gano cewa daga shekarar 2020 zuwa 2025 an rasa rayuka akalla 1,600 a sanadiyyar hatsarin jiragen ruwa a sassa daban na Najeriya.
- 2020: Mutane 350 sun mutu a fadin Najeriya
- 2021: Mutane 281 sun mutu, ciki har da 156 a Warrah, Kebbi
- 2022: Mutane 313 sun mutu
- 2023: Fiye da mutane 300 sun mutu, a cewar CILT Nigeria
- 2024: Mutane 326 sun mutu, Niger da Kwara sun fi yawan mace-mace
- Yuli 2025: Mutane 34 sun mutu.
Shugaban HYPPADEC, Hon. Joseph Terfa Ityav, ya danganta hadurran da lalacewar jiragen ruwa, cika da kaya, rashin rigar kare rai da kuma itatuwan da ke cikin ruwa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link