Jam’iyyar NNPP Za Ta Yi Gagarumin Tasiri A Zaben 2027 – Kwankwaso


A gabanin zabukan 2027, ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a shekarar 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yi alkawarin cewa jam’iyyar za ta yi gagarumin tasiri a lokacin zaben 2027.

A yayin da yake Magana da manema laarai a Abuja a taron kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyya, Kwankwaso wanda shi ne jagoran kuma tsohon gwamnan Jihar Kano ya yaba da tsarin jam’iyyar da ayyukanta, yana mai cewa ita ce daya daga cikin jam’iyyun da suke da tasiri da yin aiki sosai a kasar nan.

  • Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno
  • Sarki Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe kwana 25 A Hannun Masu Garkuwa A Kwara

Yayin da yake taya sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupetan murna, ya nuna fata cewa zai yi nasara a aikinsa, Kwankwaso ya yaba wa mambobin jam’iyyar don gudanar da zabukan reshen jam’iyyar a fadin kasar cikin ladabi da tsari, yana mai cewa jam’iyyar ta shirya sosai don tunkarar zaben 2027.

Ya kuma gode wa gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, saboda goyon bayansa da kyakkyawan aiki, haka nan ya yi kira ga mambobin jam’iyya su ci gaba da zama masu himma da hadin kai, ya jaddada cewa hadin kai da fahimtar juna da jajircewa sune makullin nasarar jam’iyya.

Tun da farko a jawabinsa, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dakta Ajuiji Ahmed wanda kuma ya samu nasarar yi tazarce na ci gaba da shugabancin jam’iyya, ya ce jam’iyyar ta tsaya tsayin daka duk da kokarin kawo cikas ga ayyukanta, amma hakan haskaka nasarorin jam’iyyar, inda ya jaddada shugabanci mai cike da hadin kai tsakanin mambobi, da kuma kokarin yin biyayya ga muhimman ka’idoji.

Ya yaba wa gwamnan jam’iyyar a Jihar Kano saboda samar da abubuwan more rayuwa na ilimi da lafiya da gine-gine da ci gaban Dan’adam, yana mai cewa gwamnan ya daga tutar jam’iyyar sosai.

Ahmed wanda ya kuma ya ba wa jagoran jam’iyyar na kasa tare da siffanta shi a matsayin gwarzon siyasa a Kano da ma Nijeriya gaba daya. Ya yi kira ga mambobin jam’iyya su ci gaba da mayar da hankali kan manufofinsu, yana mai cewa jam’iyya na goyon bayan jaronta na kasa da gwamnanta wajen samun nasara a zaben 2027.

Ahmed ya kuma yi gargadi kan yunkurin tilasta wa Nijeriya ta koma tsarin jam’iyya daya, yana mai cewa irin wadannan kokarin zai kai ga ruguza kasar nan baki daya.

Maganganun shugaban NNPP sun zo ne a tsakiyar jita-jitar da ke yawo game da makomar jam’iyyar da rawar da take takawa a siyasar Nijeriya.

A cikin jawabinsa, sakataren jam’iyyar na kasa, Oladipo Olayuku, ya yaba wa shugabannin jam’iyyar ciki har da Sanata Rabiu Musa Kwankwasa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, saboda rawar da suka taka wajen sauya fasali jam’iyyar wanda ta yi tasiri a kasa baki daya.

Olayuku ya cewa lokacin da shugaban jam’iyyar na yanzu ya karbi mulki a shekarar 2022, NNPP ba a san shi sosai ba, amma ta hanyar kokarinsu, ya zama sananne a ko’ina kuma jam’iyya ce ta kasa baki daya, kamar yadda ya yaba da yadda jam’iyyar ta yi a zaben 2023, duk da cin amanar da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi, kuma ya yaba da gwamnan Jihar Kano da sauran jami’an da aka zaba saboda kyakkyawan aikinsu.

Olayuku wanda ya yi godiya ga bangarenn shari’a saboda kin amfani da su wajen keta tsarin gudanarwar jam’iyya, ya bayyana cewa jam’iyyar ta sake duba kundin tsarinta, ta canza tambari da takenta da tutarta, kuma tana shirye-shirye tun karar zaben 2027.

Olayuku ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyya su yi aiki tare, su manta da batutuwan rashin jituwa, su kuma goyi bayan sabon shugabanci da za a bayyana a taron kasa na jam’iyyar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *