Da Sahalewar Nijeriya Bayan Samun Bayanan Sirri Amurka Ta Kai Hari — Tuggar

[ad_1]

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa harin saman da Amurka ta kai a ranar Alhamis a Nijeriya an yi su ne da cikakken sani, da goyon baya bayan samun bayanan sirri, da kuma sahalewar Gwamnatin Tarayya.

Tuggar ya bayyana haka a ranar Juma’a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce hukumomin Nijeriya sun kasance cikin tattaunawa kai tsaye da Amurka kafin a aiwatar da harin. Ya ce ya tattauna da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, na tsawon mintuna 19 kafin harin, sannan kuma mintuna biyar kafin a kai harin.

  • Harin Sama Na Amurka Mataki Na Farko Ne Na Dakatar Da Ta’addanci A Nijeriya — Moore
  • Tuggar Ya Yi Alhinin Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Mu ne muka bayar da bayanan sirri,” in ji Tuggar. “Na tuntubi Shugaba Bola Tinubu bayan tattaunawar, kuma ya ba da amincewarsa kafin a aiwatar da aikin.”

Ministan ya jaddada cewa Nijeriya na aiki da dukkan ƙasashen da ke da niyyar yaƙi da ta’addanci ba tare da la’akari da addini ko nau’in ta’addancin ba, yana mai cewa harin ya nuna ƙudirin gwamnatin Tinubu na ɗaukar tsauraran matakai wajen magance matsalar tsaro.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *