Yadda gobara ta ƙone kasuwa cikin dare a Kano

[ad_1]



Wata gobara da ta tashi cikin dare ta ƙone kasuwar sayar da kayan ɗaki ta Sabuwar Lale da ke unguwar Tal’udu a Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Shaidu, sun ce gobarar ta tashi da misalin karfe 2:30 na dare, inda ta bazu cikin sauri a kasuwar tare da ƙone shaguna da dama kafin isowar jami’an Hukumar Kashe Gobara ta jihar.

Wani ɗan kasuwa da shagonsa ya ƙone ƙurmus mai suna Bashir Ustaz, ya bayyana yadda ya ji lokacin da ya tarar komai nasa ya lalace.

“Misalin ƙarfe 3 na dare aka kira wai na zo kasuwa wuta tana ci. A gaskiya ina zuwa abin da na gani sai rufe idona na yi.

“Komai wutar ta cinye shi ga shi nan. A jiya (Asabar) idan mutum zai wuce sai yana neman a buɗa masa hanya. Amma yanzu gashi komai ya ƙone,” in ji shi.

Mataimakin shugaban kasuwar, Adamu Mansur wanda aka fi sani da Madaki, ya bayyana yadda suka wayi gari da gobarar.

“Wutar tun kusan ƙarfe 2:30 ta ke ci ha zuwa Asuba. Muna fatan Allah Ya tabbatar mana da alheri a bayan wannan gobara,” in ji Madaki.

Ya ƙara da cewar: “Mu kanmu ba za mu iya bayyana asarar dukiyar da muka yi a wannan kasuwar ba.

“A iya shagona akwai kayan mutane ya fi saiti 40 da za a ɗauka yau, akwai sait huɗu da za a ɗauka ya fi na miliyan biyar. Akwai saiti na uku ya fi na miliyan huɗu.”

Mataimakin shugaban kasuwar ya ce sun miƙa lamarinsu ga Allah, kuma suna kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su tallafa musu duba da irin asarar da ta same su.

Aƙalla shaguna 11 da wasu shaguna 20 na wucin gadi ne suka ƙone kurmus, lamarin da ya lalata kayan ɗaki, kayan aiki da sauran kayayyaki na miliyoyin kuɗi.

Jami’an Hukumar Kashe Gobara, sun yi ƙoƙarin shawo kan gobarar na tsawon sa’o’i, kafin daga bisani suka samu nasarar kashe ta bayan sallar Asuba.

An tafka asarar dukiya a gobarar, amma ba a samu asarar rai ba.

Sai dai ’yan kasuwar da abin ya shafa sun ce gobarar ta tsayar musu da hanyar dogaro da kai, sakamakon asarar da suka tafka mai yawa.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wata sanarwa daga Hukumar Kashe Gobara ta jihar, game da lamarin.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda gobarar ta ƙone kasuwar:


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *