Kotu Ta Wanke Abba Kyari A Shari’ar Bayyana Kadarori, Ta Soki NDLEA
[ad_1]
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sallami tare da wanke dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yansanda (DCP), Abba Kyari, daga tuhume-tuhume 23 da ake masa kan zargin rashin bayyana kadarori da NDLEA ta shigar.
A hukuncin da Mai Shari’a James Omotosho ya yanke ranar Alhamis, ya ce masu gabatar da ƙara sun gaza gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa Kyari da sauran waɗanda ake tuhuma tare da shi.
- Ronaldo Ya Fice Daga Saudi Arabia Yayinda Hare-Haren Kasar Iran Suka Zafafa
- NDLEA Ta Cafke Mai Safarar Kwayoyi Da Ta Yi Cikin Bogi
An gurfanar da Abba Kyari tare da ‘yan uwansa biyu, bisa zargin bayar da bayanan ƙarya domin ɓoye asalin wasu kadarori da ake dangantawa da jami’in ɗansandan.
Mai shari’ar ya bayyana cewa NDLEA ba ta gabatar da isassun hujjoji da za su nuna cewa kadarorin da aka ambata a cikin tuhume-tuhumen mallakin Kyari ne ba.
Hukuncin kotun ya kawo ƙarshen shari’ar da ta ja hankalin jama’a, inda ya wanke Abba Kyari daga dukkan zarge-zargen da ake masa.
[ad_2]
Source link