Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

[ad_1]


Mai magana da yawun Ofishin kula da harkokin Taiwan na Majalisar gudanarwar kasar Sin ya bayyana a jiya Talata cewa, binciken da ‘yan sanda ke yi a kan Shen Pao-yang, mai ra’ayin tawayen ‘yancin kai na Taiwan bisa zargin ballewa daga kasa, mataki ne mai adalci da ya wajaba a dauka don kare hadin kan kasa.

Mai magana da yawun Chen Binhua, ya yi wannan bayani ne bayan ‘yan sanda a birnin Chongqing sun sanar da kaddamar da binciken miyagun laifuka kan Shen, bisa zarginsa da aikata wasu dabi’u na neman ballewa, ciki har da kafa kungiyar ‘yan aware mai suna “Kuma Academy”.

Chen ya kara da cewa, “Manufar kai kakkarfan farmaki da kuma hukunci mai tsanani a kan tsirarun ‘yan tawayen neman “’yancin kan Taiwan” a karkashin doka, ita ce kare muradu da walwalar galibin al’ummar yankin Taiwan da kuma kare ikon mallakar kasa da martabar iyakokin kasa.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *