Abiya Ya Zama Shugaban Jam’iyyar NNPP A Kano

[ad_1]

An naɗa Hon. Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, bayan tsige tsohon shugaban jam’iyyar, Hashimu Dungurawa.

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar a matakin jiha ne, ya amince da naɗin, bayan taron gaggawa da suka yi a Kano a ranar Talata.

  • Jami’ar MDD: Kasar Sin Babbar Ginshiki Ce Ta Cinikayyar Duniya
  • AFCON 2026: Nijeriya Ta Ƙare A Matsayi Na Ɗaya A Rukunin C

Shugabannin jam’iyyar sun ce an tsige Dungurawa ne bisa zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya.

Abiya ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa a dunƙule tare da bin jagorancin jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Har yanzu ba a tabbatar ko shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa za su amince da wannan sauyin shugabanci ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *