An tsare mafarautan Kano 6 a kurkukun Imo wata 11 ba tare da shari’a ba
[ad_1]
Mafarauta shida ’yan asalin jihar Kano sun koka kan tsawon lokacin da suka shafe a tsare a kurkukun jihar Imo ba tare da gurfanar da su a gaban kotu, tuhuma ko bayar da belinsu ba.
Mutanen, waɗanda suka dage cewa ba su da laifi, sun ce an kama su ne a watan Janairu a wani daji da ke kusa da Owerri, babban birnin jihar Imo.
A cewarsu, wasu ’yan bangar yankin ne suka kama su, inda suka zarge su da kasancewa masu garkuwa da mutane.
Sai dai duk da iƙirarin rashin aikata kowanne irin laifi da kuma rashin wata hujja da ke nuna aikata laifin, har yanzu suna tsare a gidan gyaran hali na Owerri.
Ɗaya daga cikin waɗanda ake tsare da su, Faisal Auwal, ya bayyana yadda lamarin ya faro da yadda suka shafe watanni 11 a tsare ba tare da shari’a ba.
Ya ce suna kan farautar ne lokacin da ’yan bangar suka cafke su, suka zarge su da fashi da makami da garkuwa da mutane.
“Suna zarginmu da fashi da makami da garkuwa da mutane, amma sun ƙi kai mu kotu,” in ji Auwal.
“Abin da aka kama mu da shi kawai sandunan farauta ne, sai wuƙar yanka naman farautar sai guraye a jikinmu da kuma garin ƙwaƙi. Shi kenan. Babu makami ko ɗaya.”
Ya lissafa waɗanda aka kama da suka hada da shi kansa da Idris Abdullahi, Isah Suleiman, Najib Fako, Nasiru Sa’idu da Najib Abdullahi, Muhammad Abdullahi.
“Mun shaida musu cewa mu mafarauta ne kawai, amma suka nace suka kama mu,” in ji shi.
Tsarewa ba tare da tuhuma ba
Masana shari’a sun ce tsawon lokacin da aka tsare su ba tare da kai su kotu ba ya saba wa dokar ACJA ta 2015, wadda ta iyakance lokacin da za a iya tsare mutum ba tare da shari’a ba.
A ƙarƙashin sashe na 296 na dokar, wanda aka tsare ta umarnin kotun majistare ba za a iya riƙe shi fiye da kwanaki 14 a lokaci guda ba, tare da yiwuwar ƙarin kwanaki 14. Bayan kwanaki 28, doka ta tanadi cewa dole a kai shari’ar babbar kotu ko a bayar da belin shi.
Amma mafarautan sun ce bayan kama su, an miƙa su ga ’yan sanda, waɗanda suka kai su kotun ta majistare.
Kotun ta bayar da umarnin tsare su a gidan yari. Tun daga lokacin a cewarsu, ba a shigar da wata tuhuma ba, kuma ba a tura su babbar kotun da za ta yi musu shari’a ba.
“Tun da aka fara tsare mu, alƙalin bai zauna ba tsawon fiye da watanni shida yanzu. Ba a shigar da tuhuma a kan ba. Muna buƙatar sanin makomar mu,” in ji Faisal.
Iyalan sun shiga damuwa
Tsawon lokacin tsarewar ya jefa ’yan uwan waɗanda ake tsare cikin damuwa. Mahaifin Faisal, Auwal Maigoro, ya bayyana takaici kan halin da ɗansa ke ciki.
“Ɗana yana da shekara 24 kacal kuma wannan ne karo na farko da ya taɓa zuwa kudancin Najeriya. Ko a nan Kano kafin ya tafi, ba mafarauci ba ne. Ba mu san abin da za mu yi don kubutar da su ba,” in ji shi.
Sanusi Usman, ɗan uwa ga Idris Abdullahi, shi ma ya bayyana damuwarsa.
Ya ce Idris ya shafe kusan shekara guda a gidan yari, kuma duk ƙoƙarin da suka yi don kubutar da shi ya ci tura.
“Mun fara magana daga baya, amma kullum suna koka mana cewa lauyoyi suna karɓar kuɗaɗe daga gare su ba tare da samun ƙwaƙƙwarar makoma ba. Akwai ɗan uwana ma da ya kai ƙorafi ga wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam a nan Kano, wadda ta yi alƙawarin shiga tsakani, amma har yanzu babu abin da ta yi. Muna son a yi musu adalci. Idan ba su da laifi kamar yadda ake zarginsu, ya kamata a sake su,” in ji Usman.
Lauya ya tabbatar da rashin fara shari’ar
Barista Ifeanyi Chukwuocha, lauyan da ke kare mafarautan a Imo, ya tabbatar da cewa har yanzu ba a tura shari’ar a wata kotun ba.
“Har yanzu ba a tura su kotun da za ta yi musu shari’a ba. Abin da muke ta jira ke nan yanzu. Har yanzu suna tsare a gidan yari.
“An tsare su a kotun majistare, amma kotun majistare ba za ta iya shari’ar irin wannan laifi ba. Da zarar an tura shari’ar ga wani alƙali, alƙalin zai iya bayar da belinsu,” in ji shi.
Sai dai lauyan ya ce har yanzu Ma’aikatar Shari’a ta jihar ba ta ayyana kotun da za a tura su ba ballantana a gurfanar da su a can.
“Kawai ajiyarsu ake yi a gidan kurkuku,” in ji Barista Ifeanyi.
‘Ba mu aikata laifin da ake zarginmu ba’
Wani daga cikin waɗanda ake tsare da su, Idris Abdullahi, ya bayyana yadda aka kama su a wani daji da ke kusa da wani ƙauye mai suna Ilele a jihar a farkon wannan shekarar.
Ya ce ’yan banga ne suka tsayar da su, suka duba jakunkunansu, amma ba su samu komai na laifi a ciki ba.
“Daga nan ne sai suka miƙa mu ga ’yan sanda, waɗanda suka kai mu kotun da ta tsare mu. Dukkanmu muna da sana’o’inmu a nan, ba farautar ce kawai ta kai mu Imo ba, ita muna yi ne kawai don nishaɗi.
“Wasu daga cikinmu suna aiki a gidajen yin burodi, wasu kuma a kamfanonin gwangwan. Ba mu taɓa tunanin za mu shiga wannan matsala ba,” in ji shi.
Abdullahi ya ƙara da cewa wanda ya jagorance su a tafiyar mai suna Mali, wanda ɗan asalin Kano ne, ya shafe sama da shekaru 20 yana farauta a yankin ba tare da ya taɓa fuskantar irin wannan matsalar ba.
“Ko ’yan sanda sun shaida mana ba mu aikata laifi ba. An kama mu ne kawai saboda ba a yarda da mu ba. Muna roƙon a yi mana adalci,” in ji shi.
Kiran neman adalci
Mafarautan da iyalansu suna roƙon hukumomi da su shiga tsakani a lamarin don yi musu adalci.
Suna jaddada cewa tsawon lokacin da ake tsare da su ba tare da shari’a ba ya tauye ’yancinsu kuma ya katse rayuwarsu da sana’o’insu.
“Muna son a yi mana adalci. Idan muna da laifi, a kai mu kotu a tuhume mu. Idan ba mu da laifi, a sake mu,” in ji Auwal.
Da aka tuntubi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan jihar ta Imo, Henry Okoye, ya ce ba su da masaniya kan kamawa tare da tsare mafarautar a jihar.
Kazalika, duk ƙoƙarin wakilinmu na jin ta bakin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Imo ya ci tura. Lambar da aka samu daga shafin intanet na ma’aikatar ba ta shiga, rubutaccen saƙon da aka tura lambar kuma bai shiga ba. Bugu da ƙari, ba a dawo da amsa da saƙon imel ɗin da wakilinmu ya aike wa ma’aikatar ba, har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link