Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya
[ad_1]
Hukumar Kula da Ganin Wata ta ƙasar Saudiyya, ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ƙasar.
Hakan na nufin za a azumci ranar Alhamis, inda azumin watan Ramadan na bana za a cike ya zama 30 kenan.
Don haka ranar Juma’a, 20 ga watan Maris, 2026 ce za ta yi daidai da 1 ga watan Shawwal na shekarar 1447 bayan hijira.
A kan haka ne hukumar gudanarwar ƙasar Saudiyya, ta umarci jama’ar ƙasar da su cike azuminsu zuwa 30, sannan su yi idi a ranar Juma’a.
Tun a ranar Talata ne dai wasu masana Ilimin Taurari da Sararin Samaniya suka yi hasashen cewar ba za a ga jinjirin watan Shawwal ba a ranar Laraba ba, har sai zuwa ranar Alhamis.
Hukumar ta kuma ƙarfafa wa Musulmi gwiwa su yi amfani da sauran lokacin Ramadan wajen yin ibada da ayyukan alheri, tare da roƙon Allah Ya karɓi azuminsu da sauran ibadunsu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link