Mutane 4 Sun Rasu Bayan Motoci Sun Kutsa Cikin Gasar Al’adun Eggon A Nasarawa

[ad_1]

Mutane huɗu sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hatsarin mota da ya faru a yayin bikin al’adun Eggon na shekarar 2025 a garin Nassarawa Eggon dake Jihar Nasarawa. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, yayin da jerin gwanon bikin ke wucewa kusa da Makarantar Sakandaren Al’umma ta Eggon.

Rahotanni sun nuna cewa wata babbar mota ta ƙwace daga hanya, in da nan take ta kutsa cikin masu jerin gwanon ta kashe mutane uku nan take, kafin wasu motoci biyu suka sake shiga wajen hatsarin, hakan ya sanya lamarin da ya ƙara tsananta. Shaidu sun ce mutane da dama sun samu raunuka daban-daban sakamakon hatsarin.

  • Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Gabon
  • Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Nasarawa, Yahaya Sabo-Adikwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya danganta hatsarin da tuƙi cikin ganganci. Ya ce gawarwakin mamatan an kai su ɗakin ajiyar gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lafia.

A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana alhini da kaɗuwa kan faruwar lamarin, yana mai cewa rana ce mai baƙin tarihi ga al’ummar Eggon. Ta bakin Mai Taimaka Masa kan Harkokin Jama’a, Peter Ahemba, gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga Aren Eggon, da iyalan mamatan da ɗaukacin al’ummar Eggon, tare da addu’ar samun sauƙin warkewa ga waɗanda suka jikkata.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *