Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Bayyana 23 Ga Janairu A Matsayin Ranar Cin Amana

[ad_1]

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana ranar 23 ga watan Janairu a matsayin ranar cin amana bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga magoya bayan Kwankwasiyya da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Miller Road a Kano, domin nuna masa goyon baya.

  • Tawaga Ta 26 Ta Jami’an Kiwon Lafiyar Sin Ta Isa Rwanda
  • Yadda Aka Gudanar Da Gangamin ‘Detty December’ Na ‘Malta Guinness’ A Enugu Da Kaduna

Gwamnan jihar ya fice daga NNPP ne tare da ’yan majalisar dokokin jihar Kano 21, ’yan majalisar wakilai takwas, da kuma dukkanin shugabannin ƙananan hukumomi 44 a ranar Juma’a.

Da yake mayar da martani, Kwankwaso ya bayyana ficewar a matsayin cin amana, yana mai cewa wani sharhi da ya gani a shafukan sada zumunta ne ya ja hankalinsa.

“Mutane da dama na magana kan cin amana, amma wani sharhi ya ba da shawarar a ayyana 23 ga watan Janairu a matsayin Ranar Cin Amana,” in ji shi.

Ya ce ya amince da shawarar, kuma daga yanzu za a riƙa tunawa da ranar a duk shekara domin tunatar da jama’a abin da ya faru.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun ruɗani a siyasar Kano sakamakon wannan gagarumin sauyi da aka samu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *