Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

[ad_1]


Majalisar Dattawa ta tabbatar da Dr. Bernard Doro a matsayin sabon Ministan Harkokin jin ƙai da rage talauci, a yau Alhamis. Wannan na zuwa ne bayan garambawul a jadawalin ministoci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Taron tantancewar Doro bai wuce mintuna 30 ba, inda ƴan majalisar suka bayyana gamsuwa da ƙwarewarsa da kuma basirarsa ta jagoranci. Doro, ɗan asalin jihar Plateau, wanda zai zama minista na uku daga jiharsa a wannan gwamnati, ya yi alƙawarin gudanar da ayyuka bisa gaskiya da adalci.

“Zan gina tsarin jin ƙai da ya ƙunshi kowa, mai dogaro da gaskiya da ƴanci,” in ji Doro yayin zaman tantancewa.

Bayan nuna gamsuwa da takardun shaidarsa da manufofinsa, ƴan majalisar suka umarce shi da ya “take a bow” sannan suka amince da naɗinsa ba tare da wani saɓani ba.

Shugaba Tinubu ne ya aike da wasiƙar neman tantance Doro zuwa majalisar bisa tanadin sashi na 147 (2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara), inda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasiƙar a zauren majalisa kafin a miƙa ta ga Kwamitin Majalisar Duka don ɗaukar mataki nan take.

An zabi Doro ne bayan naɗin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC ta ƙasa. Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana Doro a matsayin ƙwararren masani da ke da fiye da shekaru 20 na ƙwarewa a fannoni da dama ciki har da aikin asibiti, gudanar da harkokin magunguna, da jagoranci a Nijeriya da Birtaniya.

An haifi Doro a ranar 23 ga Janairu, 1969, a Kwall, ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau. Yana da digiri a fannin magunguna da shari’a, MBA a dabarun kasuwanci na IT, da kuma digiri na biyu a fannin aikin lafiya mai zurfi (Advanced Clinical Practice).

Da amincewar da aka yi masa a yau, ana sa ran Bernard Doro zai rantse a matsayin ɗan majalisar zartarwa (FEC) a zaman majalisar ministoci na gaba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *