Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja

[ad_1]



Rahotanni sun bayyana cewa, wata gobara ta ƙone wani shagon Adidas Sports da ke cikin rukunin babban kantin nan na sayar da kayayyaki na Jabi Lake Mall, Abuja da tsakar daren Alhamis.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shagon ne kaɗai gobarar ta shafa.

An kuma samu rahoton cewa, an baza jami’an kashe gobara daga Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da na Kamfanin Berger da na hukumar kashe gobara ta Abuja da kuma jami’an ’yan sanda zuwa wurin.

A lokacin da Wakilin Daily Trust ya kai ziyara da safe zuwa wurin, an shawo kan gobarar.

Wani ma’aikaci a shagon ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na tsakar daren ranar Alhamis.

Ya ce, ba a samu asarar rai ba a wurin. Ya kuma tabbatar da cewa, “Shagon sayar da kayan Wasannin Adidas ne kawai gobarar ta shafa.”

Mai magana da yawun Hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya, Ibrahim Mohammad, ya tabbatarwa da majiyar da faruwar lamarin, amma ya ce ƙarama ce.

Ya ce, an shawo kan lamarin kuma an dawo da zaman lafiya.

Ita ma da take mayar da martani, kakakin rundunar ’yan sandan Birnin Tarayya, Josephine Adeh ta ce an tura jami’an ’yan sanda wurin da lamarin ya faru domin kare yankin da kuma hana sace-sacen jama’a.

“Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:40 na asubahi, nan take muka tura mutanenmu wurin domin su tsare wurin da kuma hana duk wani abu da ya saɓa wa zaman lafiya,” in ji ta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *