Trump Ya Yi Alƙawarin Dakatar Da Shigowar Masu Hijira Daga Matalautan Ƙasashe



Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada manufarsa ta dakatar da shigowar masu hijira daga ƙasashen masu ƙaramin ƙarfi, yana mai cewa wannan mataki wajibi ne domin tsaron ƙasa. Jawabin nasa ya zo ne bayan harbin da aka yi wa wasu Sojoji biyu a birnin Washington D.C, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaya daga cikinsu. Rahotanni sun ce wani ɗan ƙasar Afghanistan ne mai shekaru 29, wanda ya taɓa aiki tare da CIA, shi ake zargi da kai harin.

Trump ya yi iƙirarin cewa yawancin baƙin haure da ke Amurka su ne ke ƙara yawan laifuka, duk da akwai binciken da ya nuna akasin haka. Nazarin da aka wallafa a 2024 ya tabbatar da cewa babu wata alaƙa tsakanin yawan ƴan gudun hijira da ƙaruwar aikata laifuka a Amurka, yayin da wani binciken tattalin arziƙi a 2023 ya nuna cewa baƙin haure na da kashi 60 cikin 100 na waɗanda ba su da yiwuwar gurfana a gaban kotu idan aka kwatanta da ƴan ƙasar.

A cikin saƙonsa da ya wallafa a  manhajar Truth Social, Trump ya yi alƙawarin dakatar da miliyoyin izinin shiga ƙasar da gwamnatin Joe Biden ta bayar, da kuma rage tallafin gwamnati ga wadanda ba ƴan ƙasa ba. Ya kuma ce za a zartar da hukunci ga mutanen da gwamnati ta zarga da barazana ga zaman lafiya tare da korar duk wadanda ya kira “marasa dacewa da wayewar Yammacin Duniya. “



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *