Duk da Gwamnonin APC 30 Tinubu na fargaba — David Mark
[ad_1]
Shugaban Jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya bayyana dalilin da ya sa yake nuna fargaba duk da cewa yana da gwamnoni sama da 30 a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki ta APC.
Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai, inda gamayyar jam’iyyun suka nuna rashin jin daɗinsu kan cire sunayen wasu shugabannin ADC daga shafin Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Mark wanda sauran shugabannin jam’iyyar ke mara masa baya, ya yi zargin cewa akwai ƙullalliyar kafa tsarin mulkin jam’iyya guda ɗaya a Najeriya.
Mark, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kare dimokuraɗiyya, inda ya ce: “Ku tsaya tsayin daka. Ku fito ku yi magana. Ku shiga fafatawar. Ku bijire wa duk wani yunƙuri na ƙaƙaba tsarin jam’iyya guda ɗaya a Najeriya.”
“Tun daga shekarar 1999, Najeriya take ƙarƙashin mulkin dimokuradiyya. Bayan shekaru 27, mun yi tunanin za mu iya yin bikin kafuwar dimokuraɗiyya da alfahari, tare da imanin cewa zamanin mulkin kama-karya ya zama tarihi.”
“To amman abubuwan da suka faru a cikin kusan shekaru uku da suka gabata tun bayan hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki sun tabbatar da akasin haka.
Dimokuraɗiyya na ɗorewa ne kawai ta hanyar ingancin ’yancin da take bayarwa da kuma tabbatarwa, musamman ’yancin zaɓa, ’yancin shiga harkar mulki, da kuma ’yancin yin tarayya. Waɗannan ’yanci suna da matuƙar muhimmanci ga dimokuraɗiyya ta yadda idan babu su, dimokuraɗiyya za ta mutu.”
“Duk da haka, a cikin shekaru uku da suka wuce, mun ga yadda ake ta kai hari kan waɗannan ’yanci. Manufar a fili take, wato a samar da yanayin da a shekarar 2027, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kasance shi kaɗai ne zaɓin da ya rage wa mutane, duk da irin wahalhalu da kashe-kashen da ake yi a faɗin ƙasar nan.
ƙalubale biyu na tsananin fatara da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan ba su faru haka kawai ba. Sakamako ne na kai tsaye na gazawar wannan gwamnati. Sun sani cewa ’yan Najeriya ba za su so wannan ya ci gaba ba. Sun sani cewa ’yan Najeriya za su kada su a zaɓe. Shi ya sa za su yi duk abin da za su iya don ganin sun maƙale a kan mulki ta kowane hali.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link