Me Ya Sa Aka Ki Karbar Tallafi Daga Kasar Amurka?
[ad_1]
A kwanan baya, gwamnatin kasar Zambia ta sanar da kin karbar tallafin hidimar kiwon lafiya da kasar Amurka ta yi shirin samar mata. Bayan da na karanta wannan labari, na yi mamakin yadda kasar Zambia ta kyale niyya mai kyau da aka nuna mata. Sai dai daga bisani na yi kokarin tara dukkan bayanai dangane da lamarin, sa’an nan na fahimci dalilin da ya sa Zambia daukar wannan mataki. Dalilin dai shi ne Amurka ta riga ta sauya salon tallafinta, kuma niyyarta ba ta kirki ba ce.
Kasar Amurka ta tsara shirin ba da tallafin ne bisa dalilin wai taimakawa kasar Zambia a fannonin tinkarar cutar kanjamau, da zazzabin cizon sauro, da kare lafiyar jikin mata masu juna biyu, da wadanda suka haihu. Sai dai bayan zurfafa shawarwari tsakanin kasashen 2, sai niyya ta hakika ta kasar Amurka ta bayyana:
Na farko, duk da cewa kasar Amurka ta yi shirin ba da tallafin, amma ba ta son kashe kudi da yawa. Saboda haka ta rage kudin tallafin da ta yi alkawarin bayarwa daga dala biliyan 1.5 zuwa dala biliyan 1 da dan wani abu. Kana ta bukaci gwamnatin Zambia, da ta samar da dala miliyan 340 a nata bangare, da ware kudi don samar da albashi ga karin wasu jami’an lafiya dubu 40 da za su gudanar da ayyuka masu nasaba.
Na biyu, shi ne kasar Amurka na son tattaro kan bayanai, da harkar tsaro a fannin aikin lafiya na kasar da ta karbi tallafinta. Inda a cikin kundin yarjejeniyar tallafi da ta tsara, kasar Amurka ta nemi samun bayanai masu alaka da lafiyar jama’ar kasar Zambia a kai a kai, cikin shekaru 10 masu zuwa. Kana ta kayyade cewa, kasar Zambia za ta samar mata da bayanan duk wata cutar da ka iya yaduwa a cikin gidanta, cikin shekaru 25 masu zuwa.
Na uku, shi ne Amurka na son ganin yadda tallafin da ta bayar zai haifar da sabuwar moriya, wadda za ta koma aljihunta. An ce, a jajiberin ranar da za a kulla yarjejeniyar ba da tallafin, mataimakin sakataren harkokin waje na kasar Amurka Caleb Orr, ya ziyarci Zambia, inda ya gaya wa shugaba Hakainde Hichilema na kasar cewa, dole ne kasar Zambia ta ba kasar Amurka ikon musamman na samun wasu ma’adinai na kasar, irinsu tagulla, da Cobalt, da dai sauransu, kafin Amurka ta ba Zambia tallafin aikin kiwon lafiya.
La’akari da wannan yarjejeniyar tallafi mai cike da son zuciya, ta yaya kasar Zambia za ta iya yarda da ita? Don haka ba mamaki ganin yadda kasar Zambia ta ce yarjejeniyar ta saba wa moriyarta, kuma ta ki sa hannu a kanta.
Hakika, a nahiyar Afirka, ba kasar Zambia ce kadai ta nuna kin amincewa ga niyyar samar da tallafin aikin lafiya na kasar Amurka ba. Sauran kasashe irinsu Zimbabwe da Kenya, dukkansu sun janye jiki daga shirin karbar tallafi daga kasar Amurka, sakamakon yadda suke damuwa kan niyyar kasar Amurka ta mallakar bayanan lafiyar jikin al’ummunsu, da na wasu cututtuka masu yaduwa.
Dalilin da ya sa salon ba da tallafin lafiya na kasar Amurka ya sauya, shi ne sabuwar manufar kiwon lafiya a duniya da kasar Amurka ta gabatar a watan Satumban bara, wadda ta kasance irin ta “mayar da moriyar kasar Amurka a gaban ta duniya”. Sai dai yadda gwamnatin kasar Amurka take fakewa da maganar tallafin jin kai tana neman biyan bukatunta, ko Amurkawa ma ba za su iya yarda da hakan ba. Ace Robinson, shi ne shugaban kungiyar tabbatar da daidaito a fannin aikin kiwon lafiya na kasar Amurka mai taken “Equity is the Word”, ya kuma gayawa kafofin yada labaru a kwanan baya cewa, tuni gwamnatocin kasashe daban daban suka fara taka tsan-tsan a kokarin magance fadawa cikin tarkon kasar Amurka, na yin musayar wasu abubuwa ba tare da nuna adalci ba, kana a wannan karo za su kara damuwa a kan yadda ake neman keta ikon mulkin kansu. Ya kuma kara da cewa, “Ana kwatar albarkatunsu, ana kuma neman sanya su biyan karin kudi. Tabbas ba za a taba yarda da wannan shiri ba.” (Bello Wang)
[ad_2]
Source link