Musulman Ƴan Wasan Da Suke Azumi A Turai
[ad_1]
A daidai lokacin da Azumi ke ci gaba da tafiya a sassan duniya, inda Musulmai ke ƙaurace wa cin abinci ko shan ruwa daga hudowar alfijir zuwa faɗuwar rana. Wani abu da ya ɗauki hankali shi ne canjin da aka samu a duniyar ƙwallon ƙafa, inda ake ɗan dakatawa ana tsaka da wasa domin bai wa ƴan ƙwallo Musulmai dama su sha ruwa idan rana ta faɗi.
Ɗan wasa Muhammad Salah mai shekara 33 a duniya ɗan asalin Masar ne da ya kasance ginshiƙin ɗan wasa a Liɓerpool a ƴan shekarun nan kuma ɗan wasan da ya kafa tarihi da dama a gasar Premier. Salah yana ɗaya daga cikin ƴan wasa musulmi kuma an daɗe ana ganinsa yana Azumi a lokacin wasa a cikin watan Ramadan.
- Mahangar Wakiliya Mai Fasahar Wasan Kwaikwayo Game Da Dimokuradiyyar Dake Shafar Kowa Da Kowa A Nan Kasar Sin
- Kwamitin Kolin JKS Da Majalisar Gudanarwa Ta Kasar Sin Sun Taya Tawagar Kasar Ta Wasannin Olympics Na Lokacin Hunturu Murna
Ɗan wasa William Saliba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da tawagar ƴan wasan ƙasar Faransa mai shekara 24 na cikin ƴan wasan baya da suka fi ƙwazo a halin yanzu a duniya kuma Arsenal ta dogara da shi a ɓangaren tsaron baya. Shima ɗan wasa Yunus Dimoara Musah ɗan wasan ƙasar Amurka ne da aka haifa a ranar 29 ga watan Nuwamban 2002.
Yanzu ɗan wasan yana buga ƙwallo ne a ƙungiyar Atalanta da ke fafatawa a gasar Serie A, a matsayin ɗan aro daga ƙungiyar AC Milan.
Ɗan wasa Hakan Çalhanoğlu ɗan wasan tawagar ƙasar Turkiyya ne da aka haifa a ranar 8 ga Fabrairun 1994. Yanzu haka ɗan wasan yana buga ƙwallo ne a ƙungiyar Inter Milan da ke fafatawa a gasar Seria A ta Italiya.
Shima Antonio Rüdiger ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Jamus da aka haifa a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1993. Yanzu haka ɗan wasan yana buga wasa ne a ƙungiyar Real Madrid da ke Spain, kuma take fafatawa a gasar La Liga.
Matashin ɗan wasa Lamine Yamal Nasraoui Ebana ɗan wasan tawagar Spain ne da aka haifa a ranar 13 ga watan Yulin shekarar 2007. Yanzu haka matashin ɗanwasan yana buga wasa ne a ƙungiyar Barcelona da ke ƙwallo a gasar La Liga, kuma yana cikin zaratan ƴanƙwallon ke alfahari da su a harkar ƙwallo.
Tsohon ɗan wasan Manchester United da Juɓentus, Paul Labile Pogba ma ɗan wasan ƙasar Faransa ne da aka haifa a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 1993. Yanzu ɗan wasan yana buga wasa ne a ƙungiyar Monaco da ke fafatawa a gasar Ligue 1 ta Faransa.
[ad_2]
Source link