Albarkatun Daji Da Tsirrai Da Sin Ta Tattara Da Adana Sun Karu Da Kashi 180% Cikin Shekaru 5

[ad_1]

A yau Litinin ne hukumar kula da dazuka da tsirrai ta kasar Sin ta ce a yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 wato cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta dauki matakai masu amfani, don hanzarta farfado da dazuka da tsirrai. Inda karkashin hakan aka tattara, da adana jimillar albarkatun daji da tsirrai har nau’o’i 147,400, adadin da ya karu da kashi 180 cikin dari, idan aka kwatanta da karshen lokacin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 wato shekarar 2020. An yi nasarar kare muhimman nau’ikan bishiyoyi da tsirrai, da kuma albarkatun daji da tsirrai dake fuskantar barazanar bacewa.

A cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta kafa sansanonin samar da iri, na nau’o’in bishiyoyin daji sama da 1,500, da kuma sansanonin renon irin tsirrai sama da hekta 40,000 na matakai da nau’o’i daban-daban, tare da samar da matsakaicin irin bishiyoyin daji har tan 13,000, da tan 25,000 na irin ciyayi, wanda hakan ya tabbatar da bukatu daban-daban, na ingantattun iri ga manyan ayyukan kiyaye muhalli, da kuma kula da dazuzzuka bisa dorewa da sauransu. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *