Miyetti Allah ta dakatar da shugabanninta a jihohi 3

[ad_1]



Ƙungiyar kare muradun Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ayyana dakatar da wasu jagororinta daga muƙamin shugabanci a jihohi uku da ke yankin Arewacin ƙasar nan.

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren hulɗa da jama’a na ƙungiyar na ƙasa ,Ambasada Muhammad Tasiu Sulaiman da aka bayyanawa manema labarai a ranar Alhamis.

Ƙungiyar ta ce dakatarwar ya shafi shuganta a Jihar Adamawa Usman Abubakar Yirlabe da na jihar Taraba, Banmi Bello Jane, sai na Jihar Bauchi Muhammad Hussaini Buzaye.

Sanarwar ta ƙara da cewa, matakin dakatar da shugabnnin uku ya biyo bayan wasu ƙorafe-ƙorafe ne daga wasu mambobin ƙungiyar a jihohin da lamarin ya shafa da aka gabatar ta ofishin shugabanta na ƙasa Alhaji Abdullahi Bello Boɗejo, Sarkin Fulanin ƙasar Hausa.

Bayanin hakan na cewa, “Bayan nazari da kuma bincike da aka gudanar a kan ƙorafe-ƙorafen, shugaban na Miyetti Allah Kautal Hore ya umarci dakatar da shugabannin a jihohin uku domin tabbatar da yarda da kuma aminci a tsakanin mambobinta da su ke shugabanta.

Sanarwar ta yi gargaɗin cewa, duk wani yunƙurin gaza bin umarnin ko cigaba da iƙirarin jagoranci daga wajen waɗanda lamarin ya shafa, zai gamu da hukunci na hukuma.

Haka kuma ƙungiyar ta ja hankalin hukumomin tsaro a kan matakin da ta ɗaukan tare da ankarar da su cewa; Daga yanzu shugabannin uku ba sa jagorartanta a jihohin, a saboda haka duk wani mataki da su ka ɗauka baya wakiltan ƙungiyar, in ji Ambasada Sulaiman.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *