Za a yi dokar taƙaita kashe kuɗi a bukukuwan aure a Sakkwato

[ad_1]



Gwamnan Sakkwato, Alhaji Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara tsaurara aiwatar da dokar hana kashe kuɗi fiye da kima a bukukuwan aure a faɗin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake buɗe Masallacin Zawiyyar Shaikh Aliyu Bunza da Makarantar Islamiyya da ke birnin Sakkwato.

A cewarsa, ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi sakamakon yadda ma’aurata ke fuskantar matsananciyar wahala kafin ɗaura aure, lamarin da ya ƙara tsananta aure ga matasa mata da maza da suka kai mizaniyin yin aure.

Gwamnan ya ce almubazaranci da ake yi wajen shirye-shiryen aure na taka muhimmiyar rawa wajen ƙaruwa da yawan matasa marasa aure.

“Nan ba da daɗewa ba za mu zauna da masu ruwa da tsaki a jihar domin sake duba hanyoyin aiwatar da dokar hana kashe kuɗi fiye da kima a harkokin aure,” in ji Gwamnan.

Ya ƙara da cewa, da yawa daga cikin uwaye da magabata ba sa bin dokar da aka kafa, inda suke yin almubazaranci kan abubuwan da ba dole ba a yayin bukukuwan aure, abin da ya tilasta wa gwamnati shiga tsakani domin tabbatar da aiwatar da doka yadda ya kamata.

A cewarsa, almubazaranci da ake yi ya taimaka wajen ruɓanya matsalar rashin tarbiyya a tsakanin matasa da suka kasa yin aure saboda tsadar buƙatun da ake gindayawa.

Gwamnan ya yi kira ga iyaye da malamai da sarakunan gargajiya da su ba gwamnati cikakken goyon baya domin tabbatar da cewa dokar ta yi aiki yadda ya kamata.

A watan Mayun 2023 ne Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da dokar hana almubazaranci a harkokin aure.

’Yan majalisar Abubakar Shehu Yabo da Faruku Mustafa Balle ne suka gabatar da ƙudurin dokar, wanda aka tattauna a zauren majalisa tare da amincewa da shi.

Dokar ta hana almubazaranci a bukukuwan aure, zanen suna da sauran bukukuwan al’ada.

Duk da shafe sama da shekaru biyu da samar da dokar, har yanzu ba a fara amfani da ita yadda ya kamata ba a harkokin aure a jihar, lamarin da ya sa gwamnati ke ƙoƙarin dawo da jama’a kan bin dokar domin rage wahalar aure a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *