INEC Ta Amince Da Shugabancin PDP Tsagin Wike
[ad_1]
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gayyaci tsagin Jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Abdulraham Mohammed da Sanata Samuel Anyanwu zuwa wani taron tuntuɓa na jam’iyyun siyasa da aka shirya domin babban zaɓen 2027.
Tsagin, wanda Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ke goyon baya ne ya wakilci jam’iyyar da ke fama da rikici a taron masu ruwa da tsaki da hukumar zaɓe ta shirya a ranar Alhamis.
- Kotun Amurka Ta Yanke Wa Wanda Yayi Yunƙurin Kashe Trump Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai
- Nijeriya Da Faransa Sun Ƙarfafa Haɗin Gwuiwar Tsaro
In ba a manta ba, kotun tarayya da ke Ibadan, jihar Oyo, ta kori tsagin da Barr. Tanimu Turaki ke jagoranta kwanan nan.
Shugaban jam’iyyar APC, wakilan jam’iyyar ADC da David Mark ke jagoranta, da sauransu, duk sun halarci taron.
Shugaban Hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya ce a ranar Laraba a yayin da yake tattaunawa da manema labarai, a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan tuntuɓa gabanin zaɓen 2027, yace, INEC ta yanke shawarar mutunta hukuncin shari’a ne kawai.
Ya kara da cewa, Hukumar a shirye take a koyaushe ta bi duk wani hukunci na kotu da zai iya maye gurbin hukuncin da ake da shi.
[ad_2]
Source link