Firaministan Kasar Lesotho Ya Gana Da Wang Yi

[ad_1]

A jiya Asabar ne firaministan kasar Lesotho Sam Matekane, ya gana da memban hukumar siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a birnin Maseru dake kasar Lesotho.

A yayin ganawar, firaminista Matekane, ya bayyana cewa Lesotho, tana dora muhimmanci ga sada zumunta, da raya dangantakar abokantaka a tsakaninta da kasar Sin, kana tana jinjinawa kasar Sin, bisa gudummawar da take bayarwa ga raya kasashen Afirka ciki har da kasar Lesotho.

A nasa bangare, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta yabawa Lesotho bisa tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan Lesotho a fannin tabbatar da ikon mallakar yankunan kasa, da mutuncin al’ummarta, da kuma moriyar ci gabanta.

Ban da wannan kuma, Wang Yi ya zanta ta wayar tarho tare da ministan harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu Ronald Lamola, inda ya bayyana cewa, Sin na godewa Afirka ta Kudu, bisa muhimmiyar rawa da take takawa a harkokin kasa da kasa.

Shi kuwa minista Lamola, cewa ya yi Afirka ta Kudu za ta yi kokari tare da kasar Sin, wajen tabbatar da ra’ayin fadada tasirin bangarori daban daban, da tabbatar da adalci a duniya baki daya.

Haka zalika, yayin ziyararsa a nahiyar Afirka, Wang Yi ya gudanar da shawarwari ta wayar tarho tare da ministan harkokin wajen kasar Somaliya Abdisalam Dhaay, inda Wang Yi ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Somaliya, wajen tabbatar da ikon mallakar kasa, da dinkewar dukkanin kasar, da kuma cikakkun yankunan kasar, da bayyana adawa ga neman ‘yancin kan yankin Somaliland.

A nasa bangare, minista Dhaay godewa kasar Sin ya yi bisa adawarta da dukkanin ayyukan ‘yan aware da ‘yan ta’adda, da kuma taimakawa kasar Somaliya wajen samun zaman lafiya da ci gaba. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *