FRSC Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 10 A Hatsarin Kaduna
[ad_1]
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 10 tare da jikkatar wasu huɗu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Kachia–Jaba a jihar.
Kakakin hukumar a jihar, Route Commander Usman Garba, ya shaida wa manema labarai cewa fashewar taya ce ta haddasa hatsarin, wanda ya faru ne a ƙarshen mako. Ya ce mutane tara sun rasu nan take a wurin hatsarin, yayin da ɗaya daga cikin mutanen biyar da aka ceto daga baya ya rasu a Asibitin Kachia General, inda aka kai su domin kula da lafiyarsu.
- Hukumar NDLEA Ta Kama Mutum 1,130 Da Kwato Miyagun Kwayoyi Kilo 9,402 A 2025 A Kaduna
- ’Yansanda Sun Ceto Yara 76 Da Aka Yi Safararsu A Kaduna
A cewarsa, hatsarin ya faru ne a ranar Asabar, 10 ga Janairu, 2026, a garin Kwaturu da ke kan hanyar Kachia–Jaba, kuma ya shafi motoci biyu. Motocin sun haɗa da wata Tundra Hilux mai lambar rajista KWL 212 TS da kuma wata motar haya kirar Volkswagen Golf mai lambar AU 688 DAL.
Garba ya ƙara da cewa mutane 17 ne ke cikin motocin biyu a lokacin hatsarin, inda aka samu nasarar ceto mutum biyar aka kai su asibiti, amma ɗaya daga cikinsu ya rasu daga baya. Ya ce gawarwakin waɗanda suka mutu an ajiye su a ɗakin ajiyar gawarwaki na Asibitin Kachia General, yayin da FRSC ta jaddada buƙatar direbobi su riƙa kula da yanayin motocinsu domin kauce wa irin wannan iftila’i.
[ad_2]
Source link