Shugaban Kwamitin AU: Ya Kamata Kasashe Masu Tasowa Su Gabatar Da Shirin Daidaita Tsarin Duniya
[ad_1]
A ranar Juma’a da ta gabata, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka ta AU, Mahamoud Ali Youssouf, ya zanta da wakilin kafar CMG, a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ta wani shirin telabijin na musamman mai taken “Leaders Talk” da aka dauka, inda shugaban ya tabo batun kutsawa cikin kasar Venezuela, da sace shugaban kasar da uwargidansa, da sojojin kasar Amurka suka yi a kwanan baya.
Game da hakan, a cewar mista Mahamoud Youssouf, kungiyar AU ta yi kira ga kasashen duniya da su girmama ka’idojin kasa da kasa. Ban da haka, ya ce ya kamata kasashe masu tasowa su fara daukar matakai, domin gabatar da wani shiri na maye gurbin tsoffin tsare-tsaren duniya, wadanda ke bakin rushewa.
Mista Mahamoud Youssouf ya ce, lamarin da ya abku a kasar Venezuela, a ganin dimbin manazarta al’amuran duniya, tamkar matakin karshen ne na kawo karshen tsare-tsaren duniya na yanzu. Duk da haka, Mista Youssouf ya ce yana tafe da hasashe mai yakini, na fatan ganin wani sabon tsarin da zai maye gurbin tsoffin tsare-tsaren duniya dake rugujewa, kuma yana fatan ganin kasashen Afirka da kasar Sin, tare da sauran kasashe masu tasowa, sun gabatar da wani sabon tsarin kula da al’amuran duniya bisa hadin gwiwarsu.
Ban da haka, Mista Youssouf ya kara da cewa, ya kamata a girmama ka’idojin kasa da kasa, da tsarin gudanar da harkokin duniya. Saboda haka kungiyar tarayyar Afirka ta AU, sam ba ta amince da matakin tsare shugaban wata kasa ba. Kana kungiyar ta riga ta gabatar da wata sanarwa mai bayyana ra’ayinta a fili, inda ta bukaci kasar da lamarin ya shafa, da ta girmama dokokin kasa da kasa, da kariyar da aka baiwa shugabannin kasashe daban daban daga tuhumar aikata laifi.
Dangane da manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, Mista Mahamoud Youssouf ya ce, AU ta yarda, gami da tsayawa kan manufar, saboda a ganinsa, iyakokin kasar Sin na da matsayi mai matukar muhimmanci iri daya da na kasashen Afirka. Ya kara da cewa, yunkurin balle Somaliland daga kasar Somaliya da ake fuskantar a nahiyar Afirka, ya shaida bukatar kokarin dakile ra’ayin janyo baraka ga wata kasa, saboda haka, matakin kasashen Afirka na tsayawa kan manufar Sin daya taka a duniya, tamkar taimakon kansu ne ta fuskar kare hurumin yankunan kasa. Wannan dalili, a cewar mista Youssouf, ya sa kasashen Afirka ke tsayawa tare da kasar Sin a ko da yaushe, kan batun nan na kasancewar Sin daya tak a duniya. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link