Kashe-Kashe A Arewa: Gamayyar Kungiyoyi Sun Yi Zargin Akwai Hannun Kasashen Waje

[ad_1]

Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ta nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a Arewacin Nijeriya, tare da gargadin kada a yi amfani da bambancin kabilanci da addini, da kuma shigar wasu ‘yan waje cikin rikice-rikicen.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da hare-haren baya-bayan nan a jihohin Filato da Jihar Kaduna, tana mai bayyana su a matsayin mugwaye kuma marasa imani.

  • Jakadan Sin a Najeriya Ya Gana Da Shugaban Kwamitin Kula Da Makarantun Noma Da Cibiyoyin Bincike Na Majalisar Dattawa Ta Najeriya
  • Kasar Sin Ta Dakile Matsalar Safarar Yara Da Mata

Ta ambaci kashe mutane akalla 14 a Anguwan Rukuba, Karamar Hukumar Jos ta Arewa, da kuma wani hari a wurin biki a Karamar Hukumar Kagarko ta Kaduna, inda aka kashe mutane 13 tare da sace wasu da dama.

A cikin wata sanarwa da mai kula da harkokin kungiyar na kasa, Jamilu Aliyu Charanchi ya fitar, ya ce kai hare-hare kan fararen hula babban laifi ne ga bil’adama, kuma dole ne kowa ya yi Allah-wadai da hakan.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan rahotannin ramuwar gayya da wasu matasa ke yi a Jihar Filato, tana gargadin cewa: Ramuwar gayya da tashin hankali na jama’a na iya kara rura wutar rikici. Ware mutane bisa asali ko addini zai kara rarrabuwar kai. Irin wadannan matakai suna taimaka wa masu neman tayar da fitina

Charanchi ya bukaci shugabannin addini, dattawa da masu tasiri a al’umma da su yi taka-tsantsan, su guji furta kalaman da za su kara dagula al’amura.

Kungiyar ta kuma yi gargadi kan rawar da wasu ‘yan waje da kungiyoyi marasa tushe ke takawa, tana zargin cewa suna amfani da rikice-rikicen cikin gida domin cimma manufofinsu na tayar da zaune tsaye.

Ta kuma yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su: Dauki matakan gaggawa wajen kare rayuka da dukiyoyi. Inganta hanyoyin tattara bayanan sirri da kuma martani ga hare-hare. Samar da tsare-tsare na dindindin da za su magance tushen matsalar tsaro.

Haka kuma, ta bukaci hukumomin tsaro su tabbatar da kamo masu aikata laifuka tare da gurfanar da su a gaban shari’a, domin dawo da amincewar jama’a.

CNG ta jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da kira ga al’umma da su kasance masu natsuwa, bin doka, da kuma hadin kai domin gujewa fadawa cikin rikicin da zai iya raba kan jama’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *