2027: Batun Murabus Din Masu Rike Da Mukaman Gwamnati
[ad_1]
A makon da ya gabata ne, shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci wadanda ya nada, a mukaman siyasa, musamman wadanda, ke da ra’ayin tsayawa takara cewa, su yi murabus a ranar 31 na watan Maris din 2026.
Wannan umarnin na shugaban ya nuna a zahiri cewar, an riga an kada, Gangar tunkarar zaben kakar 2027 ke nan.
- Kasar Sin Ta Dakile Matsalar Safarar Yara Da Mata
- Sin Ta Kaddamar Da Shirin “Operation Sky Net 2026” Don Taso Keyar Masu Cin Hanci Da Suka Tsere
Kazalika, umarnin ya kuma cewar, yanzu a kasar, za a iya cewa, an jinge batun gudanar da harkar mulki, zuwa ga maganar tunkarar zaben gama gari, a kasar
Wannan lamarin dai, ya jefa damuwa, a zukatan ‘yan kasar, kan irin ingancin bangaren gudanar da shugabancin da ake gudanar wa a kasar.
A saboda da haka, wannan Jaridar, ta yi tsammanin wannan umarnin na shugaban, zai sanya, musamman, manyan jiga-jigan masu rike da mukaman siyasa a matakin gwamnatin tarayya, za su yi murabus, daga mukaman na su.
Babbar tambayar da ke da matukar sarkakiya kan wannan batun shi ne, shin shugaba Tinubu, zai cike gibin wadannan mukaman na ‘yan siyasar da suka yi murabus ne, ko kuwa, za a bar gurbin da suka bari ne, ba tare da ya nada kowa ba ?
Idan matsalar ta ke shi ne, ko da ma, shugaban ya nada wadanda za su cike gibin na wadanda suka yi murabus saboda rashin sanin makamar aiki a tsakanin su, zai yi matukar wuya, su iya tafiyar da bangaren gudanar da shugabancin, yadda ake bukata, musamman kari da cewa an nada su ne, a kurarren lokaci.
Bugu da kari, a gefe daya kuma, babu wani tabbacin cewa, wata sabuwar gwamnatin da ta lashe zabe, za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiyen da tsohuwar gwamnatin da ta gabata, ta faro da su, inda hakan, zai kara haifar da wani sabon rudu, a bangaren gudanar da shugabancin kasar.
Hakazalika, ma’aikatun da kuma hukumomin gwamnati, na taka muhimmiyar rawa wajen wandar da tsare-tsaren gwamnati, gudanar da ayyukan gwamnatin da kuma sanya ido kan tafiyar da tattalin arzikin kasa
Amma, idan har aka samu wani gibi, na masu rike da mukaman na siyasa, tabbas za a samu tsaikon ci gaba da wanzar da daukar matakai a bangaren gudanar da shugabancin, tare da karya lagon gudanar da sanya ido, kan tafiyar da ayyukan gwamnatin wanda a karshe, hakan zai shafi rayuwar ‘yan kasar
Kazalika, a wani bangaren, wadanda za a nada a mukaman na wucin gadi za su iya mayar da hankali a bangren siyasa kachokam, maimakon, mayar da hankali a bangren gudanar da shugabanci.
A nan, wannan Jaridar na nuna matukar damuwa, musamman kan matsalar da wannan gibin dai haifar.
Ko da yake dai, wannan umarnin na shugaban kasa, ya yi shi ne, daidai da tsarin da kundin mulkin kasar ya tana musamman duba da cewa, an kirkiro da tsarin ne, domin yin adalaci ga sauran wadanda ba su rike da mukaman gwamnati, domin kaucewa, yin amfani da karfin iko,a yayin gudanar da zabuka, a kasar.
Domin a kaucewa matsalar da wannan gibin zai haifar, akwai matukar bukatar, gwamnatin ta samar da matakan da suka kamata.
Misali, daya daga cikin matakan da ya kamata gwamnatin ta dauka shi ne, nada jami’ai a mukaman siyasa na wucin gadi wadanda kuma za su ci gaba da tafiyar da harkar shuganci yadda ya kamata ba kuma tare da, fuskantar wata tangarda ba.
Dole ne kuma a tafiyar da aikin kamar yadda dokar kasa, ta tanada.
A namu tunanin a wannan Jaridar, shawar ita ce, shugaban kasa, mai yuwa ya yi tunanin nada masu sanya ido wajen tafiyar da ma’akatun gwamnatin, mumamman domin ayyukan gwamnatin, su tafi yadda ya kamata.
Duk da cewa, wannan ba wai wani tsari ne da ya kasance a hukumance ba, amma zai iya rage tarnakin da bangaren gudanar da shugabancin kasar zai iya fuskanta dangane da wannan gibin da masu murabus, suka bari.
Hakazalika, a gefe daya kuma, a yanzu dai, fannin tattalin arzikin kasar nan, na kan wani babban siradi
duba da wasu matsaloli na cikin gida ta yake fuskanta, inda kuma, a gefe daya, na yakin da ake ci gaba da gabzawa, a Gabas ta Tsakiyawato, a tsakanin kasashen Iran da Isara’ila da kuma Amurka.
Yakin dai, ya haifar da tashin gwaron Zabi, musamman a fannin makamashi da tsadar man fetur da dangoginsa, a duniya baki daya ciki har da kasar nan.
Misali, a bangaren kasar nan, lamarin ya kara ta’azzara kuncin tattalin arzikin’ yan kasar,musamman talakawa duba da yadda lamarin ya haifar tashin farashin kayan abinci da tsadar sufuri da sauransu.
A kasa kamar irin Nijeriya wannan batun, ba abu ne da ya ke da wani sauki ko kadan ba, musamman duba da yadda hauhawan farashin kayan abinci a kasar ke dakile magidanta da dama, iya sayawa iyalansu kayan masatufi.
A yanayi irin wannan da kasar ta tsinci kanta a ciki a yanzu,kamata ya yi gwamnatin tarayya ta mayar da hankali, wajen saita fannin tattalin arzikin kasar tare da kuma samar da tsare-tsaren da za su samarwa da talakawan kasar, musamman saukin radadin rayuwar da suke ci gaba da fuskanta.
Nauyi a kan kowacce gwamnati, na ta tabbatar da an mika ragamar shugabanci daga gun wata gwamnatin zuwa wata sabuwar gwamnatin, musamman,domin a ci gaba da gudanar da harkar shuganci.
A nan, za mu iya cewa, ya zama wajibi shugaban kasa ya dauki matakan da suka kamata domin a magance wannan matsalar ta gibin da za ssmu.
Kazalika,’ yan Nijeriya na da hakkin samun shugabanci na gari, tare da kuma samar masu da ababen more rayuwa.
Nijeriya ba za ta iya rungume hannunta a bangaren abinda ya shafi tafiyar da shugabanci ba dole a san, matakan da ya kamata a dauka.
Zabuka dai, suna zuwa ne, suna kuma shudewa, amma harkar tafiyar da shugabanci, abu ne, da ya ke daram dam,wanda kuma za a rinka tafiyar da shi,dai dai da ra’ayin yan kasa.
[ad_2]
Source link