Ƴan Boko Haram Sun Nemi Dalar Amurka $300,000 Domin Sakin Mutane Biyu
[ad_1]
Wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne sun nemi kuɗin fansa dala $300,000 domin sakin mutane biyu da suka sace a watan Disambar 2025, yayin da suke kan hanyarsu daga Miringa a Karamar Hukumar Biu zuwa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Bukatar kudin fansar ta fito ne a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda waɗanda aka sace ke roƙon a kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka sace shi ne Hon. Hassan Biu Miringa, tsohon mataimakin shugaban Ƙaramar Hukumar Biu, wanda ya bayyana cikin yanayi na damuwa a cikin bidiyon, yana kira ga gwamnati da shugabannin al’umma da su taimaka wajen tabbatar da sakin su. Ya ce masu garkuwa da su na neman kuɗin fansa mai yawa kafin su sakin su.
- INEC Ta Fara Kashi Na Biyu Na Rajistar Masu Zabe
- Sojoji Sun Ceto ‘Yan Mata 12 Da Boko Haram/ISWAP Suka Sace A Borno
Rahotanni sun nuna cewa an sace mutanen biyu ne a ranar 17 ga Disambar 2025, yayin tafiyarsu daga Miringa zuwa Maiduguri. A cikin saƙon bidiyon, sun bayyana cewa ƴan ta’addan na neman dala $150,000 daga kowannensu, wanda jimillar ta kai dala $300,000, kwatankwacin kusan Naira miliyan 423.
A roƙon da suka yi, sun nemi taimakon mataimakin gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, da kuma wasu ƴan majalisa da manyan jiga-jigan yankin, ciki har da Hon. Mukhtar Betara Aliyu, da Hon. Sule Ali Rimi, da Hon. Yakubu Gambo Kimba da Alhaji Musa Dogo Biu. Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan satar mutanen da kuma buƙatar kuɗin fansar ba.
[ad_2]
Source link