An Kashe Mai Sayar Da Doya Da Ƙwai Kan N200 A Kano
[ad_1]
An kashe wani mai sayar da doya da ƙwai, Sulaiman Muhammad, bayan kaurewar rikici kan Naira 200 a Unguwar Medile Turba, da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi.
- Buhari Ya Damu Saboda Rashin Magance Matsalar Tsaro Kafin Barin Mulki – Gambari
- Kwankwaso Bai Taɓa Neman Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa Ba – NNPP
Wasu matasa ne suka je wajen Sulaiman don sayen doyar Naira 200.
Shaidu sun ce matasan da farko sun ƙi biyan kuɗin, inda suka ce ba su da Naira 200 sai babban canji.
Wani mutum ya shaida wa ‘yan jarida cewa matasan sun bai wa Sulaiman Naira 1,000, yayin da ya tafi neman canji a shagunan da ke kusa da su, sai suka kai masa hari tare da caka masa wuƙa.
“Ya rasu kafin a kai shi asibiti,” in ji shaidar.
Mazauna unguwar sun ce Sulaiman ya zubar da jini sosai, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yansandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.
[ad_2]
Source link