Atiku da Abdulaziz Yari sun yi ganawar sirri
[ad_1]
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar sirri da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari.
Atiku ya yi wannan ganawa ta sirri da Yari ne, bayan ya karɓi baƙuncin tsohon gwamnan a gidansa da ke Abuja.
Bayan ganawar tasu, wadda ba tare da shigar ’yan jarida ba, har yanzu ba a bayyana abin da suka tattauna ba.
Wannan na zuwa ne a yayin da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara ƙarfi a yayin da fitattun ’yan siyasa ke sauya sheƙa.
A kwanakin baya Atiku Abubakar ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar PDP zuwa ADC, inda ake sa ran zai nemi takarar shugaban ƙasa domin sake ƙalubalantar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya kayar da shi a zaɓen 2023.
Yari na daga cikin fitattun ’yan Jam’iyyar APC mai mulki, kuma ya yi takarar kujerar shugaban Majalisar Dattawa, amma ya sha kayi a hannun Godswil Akpabio, tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom.
Wata majiya a ADC ta ce Jam’iyyar tana tsaurara dabarunta da tuntuɓa kafin zaɓen da ke tafi.
Idan ba mamata ba, wasu fitattun ’ya’yan Jam’iyyar APC, ciki har da tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ministoci da makamantansu sun sauya sheƙa zuwa ADC.
A ɗaya ɓangaren kuma APC ta karɓi tarin fitattun ’yan siyasa da suka sauya sheƙa zuwa cikinta da suka haɗa da gwamnoni masu ci fiye da biyar da ’yan majalisar dokoki ta ƙasa fiye da 50 da sauran masu riƙe da madafun iko.
Yawan masu sauya sheƙa musamman daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC ya sa a halin yanzu APC ta fi kowace jam’iyyar rinjaye a Majalisar Dokoki ta Ƙasa da kuma yawan gwamnoni.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link