Buhari Ya Damu Saboda Rashin Magance Matsalar Tsaro Kafin Barin Mulki – Gambari
[ad_1]
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ga tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce Buhari ya yi matuƙar baƙin ciki saboda bai samu damar magance matsalolin tsaro a Nijeriya gaba ɗaya ba kafin ya bar mulki.
Da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Gambari ya ce Buhari ya samu wasu nasarori a yaƙi da Boko Haram, amma hakan bai hana shi damuwa kan yadda rashin tsaro ke ci gaba da ƙaruwa a wasu sassan ƙasar ba.
- Jaridar THE SUN Ta Karrama Gwamnan Zamfara Da Lambar Yabo Ta ‘Gwamnan Shekarar 2025’
- Kwankwaso Bai Taɓa Neman Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa Ba – NNPP
“Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi damunsa shi ne rashin yin bin da ya kamata kan matsalar tsaro kafin ya bar mulki,” in ji Gambari.
Ya ce Buhari ya fi damuwa kan matsalolin ‘yan fashi da makami, sace-sacen mutane da hare-haren da ke faruwa a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
“Halin da ake ciki a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ya dame shi sosai. Yana jin cewa ya yi duk abin da zai iya yi wa al’umma,” in ji shi.
Gambari ya kuma ƙaryata raɗe-raɗin cewa an yi barazanar juyin mulki kafin zaɓen 2023.
Ya ƙara da cewa duk da cewa Buhari yana da kyakkyawar alaƙa da sojoji, ya kasance yana mutunta dimokuraɗiyya tare da bin kundin tsarin mulki.
Gambari ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai biyayya ga mutanen da suka taimaka masa wajen gina siyasarsa.
Buhari ya yi wa Nijeriya mulki daga 2015 zuwa 2023, a baya ya mulki ƙasar a mulkin soja daga 1983 zuwa 1985.
Ya rasu a watan Yulin 2025 yana da shekaru 82.
[ad_2]
Source link