Yadda aka yi Jana’izar Sheikh Usman Rigi Rigi

[ad_1]



Daruruwan jama’a sun yi dafifi a garin Zariya domin halartar jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Khalifa Usman Idris, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi.

An gudanar da sallar jana’izar a gidan malamin da ke unguwar Kusfa, cikin garin Zariya, inda manyan malamai, shugabannin al’umma da masoyansa daga ciki da wajen Jihar Kaduna suka halarta.

Sheikh Rigi-Rigi ya rasu ne a ranar 1 ga Fabrairu, 2026, yana da shekara 57, bayan doguwar jinya. Marigayin ya bar mata hudu, ’ya’ya 37 da jikoki da dama.

Surikinsa, Malam Abubakar Ɗanyaro, ya bayyana cewa malamin ya riga mu gidan gaskiya ne da yammacin Lahadi a wani asibiti mai zaman kansa da ke Kaduna.

Sheikh Rigi-Rigi ya shahara wajen yin wa’azi cikin nishaɗi da barkwanci, lamarin da ya sa bidiyoyinsa suka yi fice a kafafen sada zumunta.

Ya ƙware a fannin Furu’a da Usul, tare da sanin sauran ilimin addini.

An fi sanin sa wajen koyar da darussa kan falalar waliyyai da almajiran Sheikh Ibrahim Inyass, da kuma iya bayyana batutuwan addini masu rikitarwa cikin sauƙi da raha.

Salon barkwanci da hikimarsa ya jawo masa masoya da dama, musamman matasa da al’ummomin ƙasa, inda ta samu mabiya a TikTok da sauran kafafen sada zumunta.

Masoyansa sun yi masa laƙabi da sunaye daban-daban kamar “Rigirigi,” “Rugum,” da “Attalili Attaghazuti,” domin nuna ƙarfin hali da wa’azinsa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *