Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya

[ad_1]

A sassa da dama na faɗin ƙasar nan, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a farkon makon da ya gabata, wanda hakan ya sa aka samu sauƙin tsananin zafin da ake fama da shi.

Rashin wutar lantarki daga tashoshin samar da wutar lantarki ya sa lamarin ya yi matuƙar ƙamari.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da ‘Yan Nijeriya 1,231 Daga Jamhuriyar Nijar A Mako Daya
  • Ba Za A Iya Daidaita Batun Mashigin Hormuz Ba Har Sai An Kawo Karshen Yaki

Matsakaicin yanayin zafi na rana a cikin watan Maris ya tashi daga digiri 33 zuwa digiri 38 a Legas da Abuja.

Ya zama wajibi a sanya gidan wutar lantarkin Nijeriya cikin kasashe masu tasowa da ke fuskantar matsalar wutar lantarki. Babu wani abu mai tabbas da ya wuce sanarwar katsewar wutar lantarki, wanda ya bar kasuwanci da gidaje wajen neman hanyoyin da za su sama wa kansu wutar ta hanyar kashe maqudan kuɗaɗen da bai kamata su kashe ba, babu gaira babu dalili.

Wane Alƙawari Tinubu Ya Yi?

A lokacin yaqin neman zaɓensa na 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, idan bai gyara matsalar wutar lantarki ba, bai kamata a sake zaben sa a karo na biyu ba. Don haka, dole ne ya yi nadama a yanzu.

Tun farkon gwamnatinsa a watan Mayu 2023, an samu katsewar wutar lantarki da dama, wanda adadin da aka bayyana a cikin shekarar 2024 ya kai sau kusan 12. Tun kafin katsewar ta yi yawa, aka ci gaba da fuskantar matsalar wuta. An danganta matsalar da raunin da ake da shi ta bangaren fasaha da kuma tsarin gudanarwa. Amma akwai abin da ake lura da shi na cewa: “Iya gwargwadon ganinka da abu, iya ƙarancin fahimtarka da shi”.

Don haka, rashin dogaro da wutar lantarkin da fadar shugaban ƙasa ta ware kimanin naira biliyan 10 a shekarar 2025, da kuma ƙarin naira biliyan 7 a shekarar 2026, don sanya sola mai amfani da hasken rana, wanda za ta taimaka wajen hana katsewar wutar lantarkin Nijeriya yadda ya kamata daga na’urar sadarwa ta ƙasa, wanda ke fama da matsalar tsufa ta layukan sadarwa da ke katsewa akai-akai, sakamakon zagon ƙasan da ake samu da rashin kulawa da kuma matsalar rashin daidaito daga mitoci.

Abin Dariyar A Kanmu Yake

A shirye ’yan Nijeriya suke, su yi izgili da munanan cututtukan da suka jima suna fama da su, haka nan idan aka zo batun maganar rashin wutar lantarki, abubuwansu na da matuƙar daura kai. Idan da za su ga wayar wuta mafi hadari (High-tension cables ) ta ƙasa-ƙasa, ba za su yi shakkar rataye kayan wankinsu a kai ba, saboda tabbacin da suke da shi na cewa, layukan wutar kawai a shimfida suke babu wutar lantarki a tare da su.

Na ga hoton bidiyo na wani maski da ake yi a kan sandar fitilun titina. Layukan babu wutar lantarki tsawon watanni, sannan kuma babu yiwuwar samun wutar.

Kyakkyawan fata da yaƙini dai, ya sake kunno kai tun a farkon gwamnatin Tinubu, a lokacin da labari ya qara tabbatar da cewa, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da ke fama da rikici a halin yanzu, ba wai kawai ya samar da wani tsari ba, har ma za a ba shi aikin tantance fitaccen ɓangaren wutar lantarki a Nijeriya. Na fahimci cewa, a cikin shirinsa, El-Rufai yana tattaunawa da Saudiyya kan yarjejeniyar zuba jarin dala biliyan 10, kafin ya samu kansa cikin mawuyacin hali.

Zuwan Adebayo

A haka Adebayo Adelabu ya ɗauki wannan aiki, aikin mai matuƙar wahala, yana mai cewa; ya gaza. Amma ba laifinsa ba ne, laifin shugaban qasa ne da ya naɗa shi da kuma majalisar dattawa ta wanke shi ko dai bisa la’akari da tarihinsa ko kuma bisa wani fata na fansa. Babu shakka, yana da hazaƙa, amma a bangaren wutar lantarki ya yi matuqar gazawa, idan aka kwatanta shi ragowar haziƙan mutane.

Mafi kyawun shekarunsa, shi ne lokacin da ya yi aiki a matsayin mai duba PWC. Ya kuma kasance Babban Darakta/CFO a bankin First Bank, sannan ya zama mataimakin gwamna a babban bankin kasar.

A al’ada, aikin banki da ya sani a wannan ɓangare ya kamata ya kasance. Amma, kasancewar Nijeriya, an fi yin la’akari da tsari iri na rabo da kuma alaƙar siyasa, shi yasa abubuwan suka sha banban.

Sannan a shekarar 2023, Tinubu ya ba shi muqamin Ministan Wutar Lantarki, bayan yunƙurin da ya yi na zama Gwamnan Jihar Oyo a Jam’iyyar Accord Party bai samu nasara ba.

Babu shakka, hakan ya qara dagula al’amura. Kazalika, za a fi tunawa da Adelabu, saboda raba rukunin biyan kuxin wutar lantarki da ya yi, wanda ba lallai ba ne hakan ya nuna ingantattun ayyukansa.

Wannan ba shi ne yake nuna cewa, Adelabu ya gaza ko bai samu nasara a aikinsa ba, rashin shaidar da zai nuna ce matsalar. Mista Dan Kunle, wani masani kan harkokin makamashi, wanda ya san tarihin wannan fanni, ya shaida min cewa;

“Babu wanda ya dage cewa, sai ministan wutar lantarki ya samo kuɗin da za a gyara wutar lantarki, amma ya rage nasa ya samar da ingantaccen tsarin da zai taimaka wajen samar da yanayin da ya dace da kuma jawo hankalin masu ruwa da tsaki.”

Adelabu, kamar sauran magabatansa, yana gudanar da ma’aikatar wutar lantarki a 2026, ta hanyar amfani da littafin aiki na 1950 na Hukumar Lantarki ta Nijeriya (ECN). Duk da haka, ko da a lokacin, lokacin da kasar ke da mutane kusan miliyan 50, Birtaniya sun san cewa; wutar lantarki na da matuƙar amfani ga tattalin arziki. Domin samun ingantacciyar wutar lantarki mai ɗorewa, dole ne su ba da fifiko, ba kawai ga manyan cibiyoyin gudanarwa ba, har ma da wuraren da za su iya biya. Shi ya sa, alal misali, ana jigilar kwal daga Enugu zuwa tashar wutar lantarki ta Ijora a Legas.

Babu Taswirar Hanya

Adelabu ba shi da taswirar hanya, idan kuma yana da ita kashi huɗu qarqashin tsarin ECN take, taswirar hanya ce da babu inda za ta je. Matsalolin da tuntuni aka saba da su, su ne dai ke ci gaba da kasancewa: waɗanda suka haxa da ƙarancin iskar gas, faduwar bishiyoyi, ƙarancin kayan aiki, basussuka masu yawa da katsewar wutar lantarki akai-akai, wanda hakan ya sa ake iya samun mega wat 4,000 kacal, maimakon mega wat 13,000.

Yayin da Adelabu ke naɗe da hannuwansa tare da ‘yan Nijeriya, wutar lantarki kuma ta yi nata waje, ɓangaren ya nutse a ƙarƙashin ƙasa, inda aka biyo shi bashin kimanin naira tiriliyan 6 a qarshen shekarar 2025, wanda hakan ya haifar da rashin biyan kuɗaɗe ga kamfanonin rarrabawa da kuma samar da wutar lantarki. Wasu daga cikin matsalolin sun riga Adelabu, amma rashin iyawarsa ce ta dame su.

Duk da haka, har yanzu yana da babban buri, amma fa ba na ya gyara kuskuren da ya yi na tsawon shekara uku yana minista ba, sai don kawai ya zama Gwamnan Jihar Oyo.

Ko shakka babu, shi kansa ya san bai yi wani abin a zo a gani a wannan muqami da aka ba shi ba. Abin kunya a wajensa sosai, domin kuwa ba zai tava goge tarihin katsewar wutar lantarkin da aka yi ta samu a lokacinsa ba. Ma’ana, babu wani abu da zai nuna face yadda kasuwancin Nijeriya ya gudana da taimakon injinan wuta na Indiya da kuma sola mai amfani da hasken rana na Qasar Sin.

Misalai Daga Afirka

Masar, mai yawan al’umma miliyan 110, tana da damar samun wutar lantarki kashi 100 cikin 100 na duniya, wanda ke samun tallafi ta hanyar dogaro da iskar gas mai qarfi (kashi 81) da havaka qananan hanyoyin ‘carbon’, kamar wutar lantarki.

Wannan yana tabbatar da cewa, al’umma na cikin wadata ta hanyar samun yadda suke so.

Afirka ta Kudu, tana samar da kashi 85 zuwa 90 a cikin 100 ga al’ummarta su kimanin miliyan 62, duk da tana fuskantar qarancin wutar, sakamakon bashin Eskom da tsufan da kayan aikin suka yi da kuma rashin kula, duk da yawan jama’an da ake da su.

Ghana ta kai kashi 88 zuwa 89 cikin 100 da ke da mutane miliyan 34, birane suna samun kusan kashi 99 cikin xari, yayin da yankunan karkara kuma a kan xan samu matsala lokaci bayan lokaci.

Kasar Kenya na da kusan kashi 76 cikin 100, wadda ke da al’umma miliyan 56, inda ta yi fice a birane da kashi 97 na wutar lantarki. Wutar ba ta wadata a qauyuka ba, koda-yake ana sa ran samun wadatuwarta nan da 2030.

Idan aka kwatanta da qasashen da ke sama, kashi 57 cikin xari na ‘yan Nijeriya katsewar wutar lantarkin da ake samu yana shafar su kai tsaye, haka nan xauke wutar na shafar kashi 85 cikin xari ga matsalar mita da cin hanci da rashawa da sauran makamantansu.

Bayan kallon Adelabu a matsayin wanda ya kasa tsinana komai a shekaru biyu da suka gabata, ina yi masa fatan tafiya salin-alin, qarqashin duhun da ya samu. Amma tun da ya dage cewa, ba zai tafi salin-alin ba, kuma ya quduri aniyar ci gaba da zama, ina tunanin wani aiki ya naxa da kansa domin ja shi Jihar Oyo, don ganin yadda zai mayar da darensu rana.

Ishiekwene shi ne Babban Editan LEADERSHIP, kuma mawallafin littafin ‘Writing for Media and Monetising It’.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *