Gwaman Inuwa ya buƙaci haɗin kan ’yan Najeriya

[ad_1]



Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi ruhin haɗin kai, fata da sadaukarwa domin shawo kan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, a yayin bikin Easter na bana.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin saƙon taya murna da ya aike wa Kiristoci ta hannun, Darakta-Janar na Harkokin Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnati, Isma’ila Uba Misilli inda ya jaddada cewa Easter lokaci ne na tunani, gyara hali da kuma sabunta ƙuduri wajen gina ƙasa mai zaman lafiya da ci gaba.

Inuwa Yahaya, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), ya ce Easter na ɗauke da babban darasi na nasarar alheri a kan mugunta da kuma fata a kan yanke ƙauna, kamar yadda rayuwar Annabi Isa Almasihu ta nuna.

Ya taya Kiristoci murnar kammala azumin Lamuni cikin nasara, tare da ƙarfafa masu da su ci gaba da nuna tausayi, sadaukar da kai da kuma yi wa al’umma hidima.

A cewarsa: “Easter na nuni da soyayya, sadaukarwa da nasarar alheri a kan mugunta. Ina taya ’yan’uwanmu Kiristoci murnar wannan lokaci mai albarka.”

Gwamnan ya kuma buƙaci a ƙara ƙaimi wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da tsaro, musamman duba da ƙalubalen tsaro da tattalin arziki da ke addabar wasu sassan Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa duk da halin da ake ciki, akwai cikakken fata cewa Najeriya za ta shawo kan matsalolinta idan aka haɗa kai aka yi aiki tare.

“A halin yanzu muna fuskantar ƙalubale, amma Easter na tunatar da mu cewa fata ba ya gushewa. Da haɗin kai da imani, za mu yi nasara,” in ji shi.

Haka kuma, ya ja hankalin ’yan Najeriya da su kasance masu bin doka tare da mutunta juna, musamman yayin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027.

Ya kuma yi kira ga shugabannin addinai da su ƙara ƙaimi wajen inganta zaman lafiya da haɗin kan al’umma, ta hanyar amfani da mumbarinsu wajen faɗakar da jama’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *