Diezani Ta Kashe Fam 140,000 A Kayan Daki Masu Tsada – Kotun Birtaniya
[ad_1]
Masu gabatar da kara na Virtaniya sun shaida wa Kotun Southwark Crown da ke London cewa tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, ta kashe kusan fam £140,000 wajen sayen kayan daki na alatu da kayan ado a rana guda.
Masu gabatar da karar sun ce wannan kashe-kashen kudi ya faru ne a lokacin da ake zargin Alison-Madueke tana karvar cin hanci (alawus-alawus) daga wasu manyan mutane a masana’antar man fetur.
- Ka Manta Da Komai, Ka Bar Abba Ya Yi Wa Kano Aiki — Matar Ganduje Ga Kwankwaso
- NDLEA Ta Yi Alkawarin Kwace Kadarorin Da Ke Ba Da Mafaka Ga Dillalan Kayoyi
A halin yanzu, Alison-Madueke na fuskantar shari’a tare da jagoran kamfanin mai, Olatimvo Ayinde, da kuma dan uwanta, Doye Agama. Mutanen ukun suna fuskantar tuhume-tuhume guda viyar da suka shafi zargin karbar cin hanci. Dukkansu sun musanta laifin da ake zarginsu da shi.
A cewar masu gabatar da kara, tsohuwar ministar ta yi wadannan sayayyar ne a wani shagon kayan tarihi na alatu a birnin London, inda ta sayi fitilu na musamman da aka kera bisa oda, kayan daki masu inganci, da kuma ayyukan fasaha na ado.
An shaida wa kotu cewa ana zargin an viya kudin kayan ta hannun wasu tsaka-tsaki, va kai tsaye ta hannun Alison Madueke ba.
Lauyar masu gavatar da kara, Alexander Healy, ta fada wa alkalai cewa Alison Madueke “ta rayu cikin rayuwar alatu a London,” inda ta kara da cewa ana zargin wasu ’yan kasuwa da ke neman samun tasiri a harkar man fetur ta Nijeriya ne suka tallafa wa wannan salon rayuwa.
Ta ce ana zargin cin hancin ba a bayar da shi a matsayin kudi kai tsaye va, sai dai a matsayin kayayyakin alatu da kuma dama ta amfani da kadarori masu tsada.
Tun da farko, a ranar 27 ga Janairu, kotun ta ji cewa ana zargin tsohuwar ministar ta karbi kayayyakin alatu da kuma amfani da manyan kadarorin kasa a matsayin alawus-alawus yayin da take kan mukaminta.
Gidan talabijin na Channels, ya ruwaito cewa magoya baya daga al’ummar Ijaw a Nijeriya sun cika wurin zama na jama’a a kotun, inda da dama daga cikinsu suka yi tafiya zuwa London domin bibiyar shari’ar.
Bangaren kariya ya musanta dukkan zarge-zargen. A ranar 29 ga Janairu, Jonathan Laidlaw, lauyan da ke kare Alison Madueke, ya shaida wa kotu cewa abokiyar aikinsa va ta da cikakken iko kan bayar da kwangilolin man fetur a lokacin da take minista.
Ya yi jayayya cewa Alison Madueke ta yi aiki ne kawai a matsayin “hatimi na tabbatarwa” ga shawarwarin da hukumomi da jami’an da suka dace suka riga suka yanke, yana mai jaddada cewa ba ta yi tasiri wajen bayar da kwangiloli ba, kuma ba ta karɓi cin hanci ba.
[ad_2]
Source link