Mutum 7 sun rasu, 14 sun jikkata a hatsarin mota a Jigawa

[ad_1]



Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Yakasawa da ke kan hanyar Dutse zuwa Ringim da Taura, a Ƙaramar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.

Hatsarin ya faru ne a ranar Litinin, inda wata mota ƙirar Golf 3 ta yi karo da wata mota ƙirar Toyota Sienna.

Har yanzu ba a tantance musabbabin aukuwar hatsarin ba a hukumance, amma shaidu sun ce gudun wuce ƙima ne ya haddasa hatsarin.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa da yankin domin kula da su, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa ɗakin ajiyar gawa.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, SP Lawan Shiisu Adam ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Ya nuna damuwarsa kan yawaitar hatsarin mota a kan hanyar Dutse zuwa Ringim da Taura.

Ya ce wannan shi ne hatsari na uku da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama cikin kwanaki bakwai a wannan hanya.

Bayanan ’yan sanda sun nuna cewa aƙalla mutum 22 ne suka rasu sakamakon aukuwar hatsari daban-daban a hanyar.

Rundunar ta buƙaci direbobi da suke kiyaye dokokin hanya, su guji tuƙin ganganci, tare da tabbatar da cewa motocinsu na cikin ƙoshin lafiya a lokacin tafiya mai nisa.

Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su inganta matakan tsaro a hanya.

Su nemi hukumomi si sanya abun taƙaita gudu da ƙara sintirin jami’an tsaro, domin hana asarar rayuka a hanyar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *