Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka




Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta Super Eagles, Eric Chelle, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Nigeria za ta lashe kofin nahiyar Afrika na 2026.

Gasar da za a buga a kasar Maroko, Challe ya jadda kwarin gwiwarsa, bisa kafa hujja da zaratan yan wasan da Nigeria ta ke da su.

Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, karo na 35 daga ranar 21 ga watan Disamba da tawagogi 24 za su fafata, domin lashe babban kofin tamaulan na Afirka.

Wannan shi ne karon farko tun 1988 da Maroko ta karɓi baƙuncin wasannin babbar gasar tamaula ta Afirka da take fatan gudanar da bikin da zai ƙayatar da duniya.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *