’Yan bindiga sun kashe mutum 7, sun jikkata 11 a Kaduna

[ad_1]



Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Hari  ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, inda suka yi ta harbe-harbe.

Har ila yau, sun yi garkuwa da wasu mazauna garin, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Waɗanda suka rasu a harin sun haɗa da: Elisha Paul, Japhet Bitrus, Obadiah Joshua, Luka Augustine, Ishaya Paul, Bawa Bulus da Ezekiel Augustine.

Haka kuma daga cikin waɗanda suka jikkata akwai; Gideon Pius, Zachariah Anthony da Moses Christopher.

Sauran sun haɗa da. uhu Sunday, Christopher Ishaya Sunday, Elisha Ishaku, Clement Godday da Janet Godday, kuma dukkaninsu suna asibiti a kwance.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce: “’Yan bindigar sun kashe mutum bakwai, sun jikkata da dama sannan suka yi garkuwa da wasu.

“Kullum cikin fargaba muke kwana.”

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya ci tura, domin bai ɗaga waya ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *