Tinubu Ya Sha Alwashin Adalci Ga Waɗanda Aka Kashe A Kasuwar Neja

[ad_1]

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba Ministan Tsaro, da Babban Hafsan Tsaro, da Hafsoshin Rundunonin Soja, da Sufeto Janar na Ƴansanda da Darakta Janar na Hukumar DSS umarnin gano wa tare da cafke waɗanda suka kai harin Kasuwar Daji a Jihar Neja, domin a gurfanar da su cikin gaggawa a gaban shari’a. Haka kuma, ya umarci hukumomin tsaro da su hanzarta ceto dukkan mutanen da aka sace.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayar da umarnin ne a ranar Lahadi biyo bayan kisan gillar da ƴan ta’adda suka yi wa mazauna wata kasuwa a Jihar Neja. Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta’addan na cikin waɗanda ke tserewa daga jihohin Sokoto da Zamfara bayan harin saman da Amurka ta kai a jajibirin Kirsimeti.

  • Jihar Neja Ta Buɗe Makarantu Bayan Ceto Ɗaliban Da Aka Sace

Shugaban kasar ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa al’ummar Kasuwan Daji da kuma sace mata da kananan yara. Ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da jajantawa Gwamnati da al’ummar Jihar Nijar bisa wannan mummunan lamari.

Tinubu ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa ya umurci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu a yankunan da ke cikin barazana, musamman kusa da dazuzzukan da ke zama mafakar masu aikata laifuka. Ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su kasance masu hadin kai da jajircewa, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da za a tsaya tsayin daka domin murkushe ’yan ta’adda da dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da abin ya shafa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *