Kwankwaso Ba Shi Ne Jagoran Jam’iyyarmu Ta NNPP A Kano Da Ƙasa Ba – NNPP
[ad_1]
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙasa a shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Sani Danmasani, ya bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba shi ne jagoran jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ko a matakin ƙasa baki ɗaya ba.
Danmasani ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya yi karin haske kan matsayar jam’iyyar dangane da rikicin shugabanci da NNPP ke fuskanta a ‘yan kwanakin nan.
- Jaridar THE SUN Ta Karrama Gwamnan Zamfara Da Lambar Yabo Ta ‘Gwamnan Shekarar 2025’
- Kwankwaso Bai Taɓa Neman Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa Ba – NNPP
A cewarsa, shugabanci halastacce na NNPP yana hannun Dr. Boniface Aniebonam, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar, tare da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Dr. Agbo Major.
Ya bayyana matuƙar damuwa da yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke ci gaba da bayyana Kwankwaso a matsayin jagoran NNPP, duk da cewa, a cewarsa, an kore shi daga jam’iyyar bisa zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa dokokin jam’iyya. Danmasani ya kara da cewa kotuna da dama, ciki har da Babbar Kotun Jihar Abia da kuma Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, sun riga sun tabbatar da korar Kwankwaso da wasu daga cikin mabiyansa daga jam’iyyar.
Danmasani ya kuma bayyana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayar da umarni na hana Kwankwaso da tawagarsa yin hulɗa da hukumar, har sai an kammala sake bitar shari’a da ke gudana.
Ya jaddada cewa INEC ba ta da hurumin tantancewa ko naɗa jagororin jam’iyya, yana mai kira ga manema labarai da masu sharhi kan siyasa da su daina danganta Kwankwaso da matsayin jagoran NNPP, domin hakan na haifar da ruɗani ga jama’a.
A ƙarshe, Danmasani ya ce wannan bayani ya zama wajibi ne domin kare gaskiya, daidaita fahimtar jama’a, da kuma guje wa rikice-rikice, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauyen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
[ad_2]
Source link