Yadda Aka Gudanar Da Taron Cikar Hadiza Bala Usman Shekara 50 A Duniya
[ad_1]
A ranar Talata 13 ga watan Janairu 2026 ne ƴanuwa da abokan arziƙi suka taru a babban ɗakin taro na Hillton Hotel Abuja inda suka yi gangamin taya Hajiya Hadiza Bala Usman, mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Shawara a kan Manufofi da Tsare-tsare murna cika shekara 50 a duniya.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya jagoranci taron, a ciklin jawabinsa ya bayyana Hadiza Bala Usman a matsayin wata jaruma kuma kallabi a tsakanin rawunna inda ya bayyana ta a matsayin wadda ta gudanar da aikinta na gwamnati da gaskiya da riƙon amana, ta kuma zama abar koyi ga dukkan mata musamman daga arewacin Nijeriya dama ƙasa baki ɗaya.
- Shugaba Xi Jinping Ya Mika Sakon Jaje Ga Takwaransa Na Switzerland Bisa Afkuwar Bala’in Gobara
- Na Ɗauki Harkar Fim Tamkar Aikin Gwamnati — Maryam Usman
Ya ce, “tabbas Hadiza ta samar wa kanta gurbi a kundin tarihin gudanar da ayyuka a ƙasar nan, saboda yawancin manyan ƙudurorin a gwamnatin nan ke aiwatarwa suna fitowa daga irin shwarwarin da ke fitowa daga ofishinta”
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce, “Hadiza Bala Usman ta samar wa kanta wannan sunan ne ta hanyar sadaukarwa, gaskiya da riƙon amana a dukkan wuraren da ta yi aiki” ya ce hakan abin a yaba ne musamman ganin daga ɓangaren ƙasar nan da ta fito inda mata basa samun cikkaken damar bayyana irin baiwa da basirar da Allah Ya basu.”
Ya kuma jaddada cewa, waɗannan nasarori da Hadiza ta samu ba bisa haɗari ba ne kuma ƴan Nijeriya na nan suna sa ido tare da fatan Allah ya cika mata dukkan burinta na alhairi, daga ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya ƙara mata tsawon rai cikin ƙoshin lafiya da ƙaruwar arziƙi.
Tun da farko, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya ce, tabbas Hadiza Bala Usman ta zama jagora kuma manuniya abar koyi ga dukkan matan Nijeriya. Ya kuma umarce ta da ta ci gaba da tsayuwa wajen kare ƙudurorin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ƙara da cewa, rayuwarta a nan gaba zai ƙara bayyana irin baiwar da Allah ya yi mata, ‘Za mu ci gaba da sa ido a kan irin gudummawar da “Za ki ci gaba bayarwa ga ƙasarmu Nijeriya”.
A nasa jawabin, Shugabhan Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa, an gudanar da taron ne domin jinjinawa ga irin gaggarumnin gudummwar da Hadiza bayar ga tattabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, gudummwa ne yawancin ƴan Nijeriya basu sani ba saboda yawancin gudummawar daga bayan fage take bayar da su, haka kuma ya ƙara wa tafiyar gwamnatin Tinubu mutumci da a idon al’ummar ƙasa dama na ƙasashen waje.
Gbajabiamila ya bayyana irin gaggarumin ayyuka da sake fasalin da ta gudanar a lokacin da take shugabantar Hukumar Jirage Ruwa ta Nijeriya (NPA), inda ta kasance mace ta farko data jagoranci hukumar. Ya ce tabbas a Nijeriya ba za a taɓa mantawa da irin ayyukan alhairin data gudanar ba inda ta farfaɗo da mutuncin hukumar a idon duniya.
Haka kuma a nashi jawabin, Ministan Ci Gaban Matasa, Ayodele Olawande, ya ce, Hadiza Bala Usman ta yi fice a ɓangaren samar da ci gaban mata da matasa, ana iya ganin haka ne musamman a irin yadda ta jagoranci fafutukar nemo ceto ƴan matan nan da aka sace a shekarun baya inda ta ƙirƙiro da tafiyar ‘BRING BACK OUR GIRLS’.
A jawabinta, Shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA, Hajiya Zubaida Umar Abubakar, ta bayyana Hadiza Usman a matsayin ƙawa wadda ta sani na tsawon fiye da shekara 30, ta ce a tsawon waɗannan shekarun ta santa ne a matsayin mai gaskiya da riƙaon amana tare da taimakon al’umma a duk inda ta samu kanta. “Wannan haka yake a rayuwarta na aikin gwamnati da rayuwarta na ƙashin kanta”.
Shugaban Hukumar Sauya Fasalin Ayyukan Gwamnati, Dr. Joe Abah ya gabatar da muƙala mai taken “Leadership Deliɓery and the Courage to Serɓe,” a wajen taron, inda bayyana cewa, yin aiki a matsayin bnabban ma’aikacin gwamnati a ƙasar nan a halin yanzu wani babban baiwa ce da ba kowa yake samu ba, a kan haka dole duk wanda ya samu wannan damar ya tabbatar da ya yi ayyukan da za su inganta rayuwar al’ummar ƙasa.
Ya bayyana cewa, a kwai manyan darussa a rayuwar Hadiza musamman a kan yadda ta gudanar da harkookin ayyukanta na gwamnati, “musamman a irin wannan lokacin ake yawo labaran ƙaryan kurege a faɗin ƙasar nan’.
Ya lura da cewa, harkar shugabanci na da matuƙar wahala, domin mutane basa iya ganin ƙoƙarinka har sai ka bar muƙamin da kake a kai amma ita Hadiza Bala Usman tun kafin ta bar muƙaman ta ake ganin irin yadda take bayar da gudummawa a ɓangarori da dama na rayuwar al’umma da kuma gudummwarta a wajen inganta ayyukan gwamnati.
A nata ɓangaren Hajiya Hadiza Bala Usman, ta bayyana jin daɗi da godiyarta ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima a kan yadda ya samu lokacin halartar taron taya murna duk da ɗimmbin ayyuykan da ke gabansa, ta kuma miƙa godiyarta ga Shugaba Tinubu da Mataimakinsa a kan yadda suka bata dama bayar da gudummwarta a wannan gwamnatin da kuma yadda ta samu damar bunƙasa rayuwarta.
Ta bayyana irin yadda ta bayar da gudummwa a shirye-shiryen tsara zaɓuɓaka tun a shekarar 2015 da kuma irin yadda ta gudanar da ayyukanta a lokacin da take shugabancin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa NPA. Ta ce ta nan a kan aƙidarta na tabbatar da bunƙasa rayuwar al’umma musamman ta tsarin shugaba Tinubu na ‘Renewed Hope Agenda’
An dai haifi Hadiza Bala Usman ne a ranar 14 ga watan Janairu 1976 a garin Zariya ta Jihar Kaduna ga iyalan shaharren malamin tarin n nan na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Dakta Bala Usman, inda ta samu horo na musamman na zama tsayayyiya mai gudanar da harkokinta cikin gaskiya da riƙon amana. A tsawon shekarun ta samu nasarar samun ci gaba a harkokin ayyuklan gwamanti ta kuma zama abar koyi ga mata na zamaninta.
Ta gina harkar karatunta ne daga Jami’ar Ahamdu Bello Zariya inda ta karanta harkokin gudanar da kasuwanci ‘Business Administration’ kafin ta wsuce Jami’ar ‘Uniɓersity of Leeds’ da ke Birtaniya inda ta samu babban digirinta a na ne ta ƙara samun ƙwarewar ɓangaren shugabanci da tafiyar dea al’umma.
Hadiza ta fara aikin gwamnati ne a hukumar (BPE) daga nan kuma ta zama mataimakiya ta mussamman ga Ministan Babban Birnin tarayya Abuja.sunan ta ya yi fice ne a shekarar 2014 a lokacin da suka ƙirƙiri gwagwamaryar neman ceto ƴan matan makarantar Chibok 200 da aka sace Bring Back Our Girls (BBOG). Inda tafiyar ya zama kafar isar da saƙo ga ƴanuwa da al’umma domin ganin an sako ƴan matan waɗanda ƙungiyar Boko Haramn suka sace.
A shekarar 2016, Hadiza Bala Usman ta kafa tarihi a yayin ta zama mace ta farko data riƙe muƙamin shugabar Hukumar Kula da Tashosin Jiragejn Ruwan Nijeriya (NPA), wanda ɓangare ne maza suka mamaye a shekarun baya. Za a ci gaba da tunawa da irin ayyukan alhairin da ta gabatar a NPA a shekaru masu zuwa.
[ad_2]
Source link