Mun kori Falasɗinawa sama da dubu 250 daga Gaza — Isra’ila

[ad_1]



Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasarar korar Falasɗinawa sama da mutum 250,000 daga birnin Gaza tun bayan da suka fara zafafa kai hare-hare a yankin.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da jami’an Falasɗinu suka ce da dama sun gaza ficewa daga kudancin ƙasar saboda cunkoso.

Mai magana da yawun sojojin Avichay Adraeeya wallafa haka a shafin X, yana cewa fiye da kashi 1 bisa huɗu na waɗanda suka rage a Gaza sun gujewa birnin don kare lafiyarsu.

Sai dai, Hukumar Tsaron Farar Hula ta Gaza, ta ba da rahoton cewa adaɗin waɗanda suka samu nasarar tsarewa bai wuce mutum dubu 70 ba.

Daƙile kafofin yada labarai a Gaza da matsalolin shiga yankunan ya sa AFP ba ta iya tabbatar da bayanan da sojoji ko kuma na tsaron farar hula suka bayar ba.

A jiya Asabar ce sjojin Isra’ila sun jefa wasu takardu zuwa birnin suna kira ga mazauna yankunan yammacin ƙasar da su yi ƙaura, yayin da jami’an tsaron farar hula suka ba da rahoton cewa Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasta cewa, a ƙarshen watan Agusta kimanin Falasɗinawa miliyan ɗaya ne ke zaune a cikin birnin Gaza da kewayen, inda ta ce ana fama da yunwa bayan da aka kwashe watanni ana fama da munanan yanayi.

MDD da wasu manyan ƙasashen sun buƙaci sojojin da su yi watsi da shirinsu na ƙwace birnin, suna masu gargaɗin bubu abin da hakan zai haifar face sake tsananta al’amuran jinƙai a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *