Masu tunanin rusa Iran ba su da masaniya a kan tarihi  — Pezeshkian

[ad_1]



Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya ce duk wanda ke tunanin zai iya rusa ƙasar Iran yana cikin ruɗani da rashin sanin yadda al’amuran duniya suka wakana tsawon shekaru.

Pezeshkian ya bayyana cewa tarihin duniya ya nuna babu wata ƙasa ko wata daula da ta amsa sunanta da ta taɓa iya goge sunan Iran.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Pezeshkian ya ce duk masu wannan tunani to tabbas ba su da masaniya a kan tarihin duniya.

“A duk wani faɗi-tashi da muka yi a tarihi, babu wata daula mai ƙarfi da ta taɓa samun nasarar goge wannan sanannen suna,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Duk wanda ke tunanin zai iya rusa Iran bai san tarihi ba. Maƙiya na gaske sun zo sun tafi, amma Iran ta ci gaba da wanzuwa.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *