Hotunan ɓarnar da harin Isra’ila ya yi a Lebanon

[ad_1]



Isra’ila ta kai wani harin sama a Kudancin birnin Beirut na ƙasar Lebanon, lamarin da ya lalata gine-gine da motoci a yankin.

Rahotanni sun ce harin ya janyo tashin hayaƙi da ya turnuƙe sararin samaniya, yayin da jami’an agaji da na tsaro suka garzaya wurin domin gudanar da aikin ceto da kuma duba ɓarnar da aka yi.

Mutane da dama sun taru a wurin harin yayin da ake ci gaba da bincike kan yiwuwar samun waɗanda suka jikkata ko suka maƙale a cikin gine-ginen da suka ruguje.

A bayan nan ne wasu rahotanni ke cewa an yi arangama tsakanin dakarun Isra’ila da mayaƙan Hezbollah a iyakar gabashin Lebanon.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasar ya ce sojojin Isra’ila sun zo wajen ne a jirage masu saukar ungulu don yin wani bincike, a nan ne dakarun Hezbollah ɗin suka cim musu harma suka kakkaɓo jirgi guda da ke ƙoƙarin tashi don arcewa.

A baya baya nan dai ministan harkokin wajen Lebanon ya zargi Hezbollah da sake jefa ƙasar cikin yakin da ba ruwanta a ciki, yana mai jaddada bukatar kungiyar ta ajiye makamanta.

Kusan mutane ɗari huɗu ne aka kashe a Lebanon tun bayan sake barkewar yaƙi tsakanin Hezbollah da Isra’ila a ranar Litinin da ta gabata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *