Ba za mu taɓa daina ƙera makaman nukiliya ba — Kim Jong Un
[ad_1]
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya jaddada matsayarsa na ci gaba da ƙarfafa shirin makaman nukiliya na ƙasarsa, inda ya bayyana Koriya ta Kudu a matsayin babbar abokiyar gaba.
Da yake magana a wani muhimmin zama na majalisar dokoki a Pyongyang, Kim ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da haɓaka makamanta na nukiliya, tare da kawar da duk wata yiwuwar tattaunawa a nan gaba da nufin hana su mallakar makaman.
Ya bayyana ikon nukiliya a matsayin ginshiƙi mai muhimmanci ga tsaron ƙasa da kuma ƙarfin gwamnati.
Kim ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa kwance damarar nukiliya na iya zama hanyar bunƙasa tattalin arziki ko tabbatar da tsaro, yana mai cewa ƙarfafa makaman nukiliya tare da ci gaban ƙasa shi ne mafita mafi dacewa.
A bayan nan ne aka sake zaɓen Kim Jong Un a matsayin shugaban Hukumar Kula da Harkokin Ƙasa, wacce ita ce mafi girman hukuma wajen tsara manufofi da gudanar da mulki a ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar, KCNA ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, 23 ga Maris.
Sai dai masu sukar gwamnati na cewa irin waɗannan zaɓe “ɗauki ɗora” a Koriya ta Arewa galibi ana tsara su tun da wuri kan wani tsari da ke kamanceceniya da na dimokuraɗiyya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link