An yi wata gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai
[ad_1]
Dubun dubatar mutane ne suka fito zanga-zanga jiya Asabar a sassan wasu ƙasashen Turai domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa, tare da kiran a kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun kuma buƙaci a saki masu fafutuka da ke cikin ayarin jiragen ruwan nan da ke hanyar kai kayan agaji ga Falasɗinawa a Gaza.
’Yan sanda a birnin Rome na Italiya sun ce kimanin mutane dubu 250 ne suka fito zanga-zanga a rana ta huɗu a jere, bayan da Isra’ila ta kama ayarin jiragen ruwa 45 da ke ƙoƙarin isa Gaza domin kai wa al’umma agaji a farkon makon jiya.
Masu zanga-zangar a birnin Rome wadda aka yi ittifakin ita ce mafi girma sun fito ne dauke da tutoci suna raira taken neman ’yancin Falasɗinu, inda wasu daga cikinsu suka yi arangama da ’yan sandan kwantar da tarzoma.
A Barcelona na ƙasar Spain kuwa, kimanin mutane dubu 70 ne suka fito, a cewar ’yan sanda, a yayin da mahukunta a birnin Madrid suka ce kusan mutane dubu 92 ne suka yi tattakin nuna goyon baya ga Falaɗinawa a babban birnin na Spain.
A birnin Dublin na ƙasar Ireland, dubban mutane sun yi tattaki don tunawa da cikar shekaru biyu na kisan ƙare dangi a Gaza.
Haka kuma, a Biritaniya, ’yan sanda sun kame kusan mutane dari biyar da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Landan na Birtaniya, wadanda suka fito tattaki domin nuna goyon bayan Falasɗinawa ƙarƙashin wata ƙungiya da aka haramta ta Palestinian Action Aide.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link