’Yan Isra’ila sun yi bore kan shirin mamaye birnin Gaza
[ad_1]
Dubban mutane sun mamaye titunan Isra’ila suna kira ga gwamnati ta kawo karshen yakin Gaza da kuma kulla yarjejeniyar sako mutanen da Hamas ke rike da su.
Zanga-zangar ta biyo bayan amincewar majalisar yakin Isra’ila da shirin mamaye birnin Gaza da kuma korar al’ummar da ke zaune a can – matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da shi.
A ranar Lahadi, dubban mutane suka hallara a dandalin “Hostages Square” da ke Tel Aviv, inda suka bukaci gwamnatin Isra’ila ta dakatar da shirinta na mamaye birnin Gaza da kumam a sako fursunonin da kungiyar Hamas ke tsare da su, wanda yawansu ya kai kusan 20.
Wannan gangami ya kasance mafi girma tun bayan fara yakin Gaza, inda aka gudanar da yajin aiki na kwana guda a fadin kasar. Yajin aikin ya shafi tituna, ofisoshi da jami’o’i a wasu sassan Isra’ila. Rahotanni sun ce an kama kusan mutane 40 a yayin zanga-zangar.
Gwamnatin Isra’ila ta soki zanga-zangar
Firai Minista Benjamin Netanyahu ya soki zanga-zangar, yana mai cewa hakan zai kara tsananta matsayin Hamas kuma zai jinkirta sakin fursunonin.
Ministan farar hula mai ra’ayin rikau, Bezalel Smotrich, ya bayyana zanga-zangar a matsayin “gamgamin cutarwa da ke taimaka wa Hamas.”
A Tel Aviv, ’yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga da karfi a gaban hedikwatar jam’iyyar Likud ta Firayim Minista Netanyaghu.
Wannan rikici ya biyo bayan taron gangami mafi girma da aka gani tun bayan watanni 22 da fara yakin. An gudanar da kananan zanga-zanga a wasu sassa na Isra’ila.
Iyalan mutanen da aka sace sun jagoranci yajin aiki
Iyalan fursunonin da ke hannun Hamas da wasu da ke adawa da fadada yakin ne suka bukaci a gudanar da yajin aikin.
Einav Zangauker, mahaifiyar Matan wanda ke hannun Hamas, ta jagoranci kungiyar “Hostage and Missing Families Forum” inda ta bukaci “yarjejeniyar da za a iya cimma da kuma kawo karshen yaki.”
Ta ce: “Muna bukatar abin da ya dace da mu — ’ya’yanmu. Gwamnatin Isra’ila ta mayar da yaki mai adalci zuwa yaki maras ma’ana.”
Ta yi wannan jawabi ne bayan fitar da wani bidiyo na danta Matan. A cikin bidiyon, ta ce: “Zuciyata na cike da kewar Matan. Ina yi maka addu’a, kai da sauran fursunoni, muna kokarin ganin an sako ku.”
MDD ta soki shirin mamaye birnin Gaza
Zanga-zangar ta biyo bayan amincewar majalisar yakin Isra’ila da shirin mamaye birnin Gaza da kuma korar al’ummar da ke zaune a can – matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta soki.
Rahotanni daga Gaza sun ce dubban mutane sun tsere daga unguwar Zeitoun da ke kudancin Gaza City, inda hare-haren Isra’ila ke ci gaba da haddasa halin “mummunan bala’i.”
Akalla mutane 40 ne suka mutu a hare-haren ranar Asabar, in ji hukumar agaji ta Gaza.
Hamas ta ce dakarun Isra’ila na kai hare-hare a gabashi da kudancin birnin Gaza City, musamman a Zeitoun.
Rundunar Isra’ila ta ce za ta fara barin kungiyoyin agaji su shigar da tantuna da kayan mafaka zuwa Gaza.
Shirin korar mutane daga Gaza City
Isra’ila na shirin korar fiye da miliyan daya daga birnin Gaza zuwa sansanonin da ke kudancin Gaza, duk da cewa ba a bayyana lokacin da za a fara shiga birnin ba.
Netanyahu na son Isra’ila ta mamaye birnin gaba ɗaya tun daga 7 ga Oktoba.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane miliyan 1.9 — kimanin kashi 90% na al’ummar Gaza — sun riga sun rasa matsugunansu.
Rahotanni sun nuna cewa akwai yawan rashin abinci a Gaza, inda masana suka yi gargadin cewa “mummunan yanayin yunwa” na faruwa a yankin.
Asalin rikicin
Yakin Gaza ya fara ne bayan harin da Hamas ta kai Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba 2023, wanda ya kashe kusan mutane 1,200 tare da sace wasu 251.
Isra’ila ta mayar da martani da hare-hare da suka kashe fiye da mutane 61,000 a Gaza, in ji ma’aikatar lafiya ta Hamas — wadda Majalisar Dinkin Duniya ke dauka a matsayin mai sahihanci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link