Rasha ta kai wa tawagar kayan agajin MDD hari a Ukraine
[ad_1]
Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki.
Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman.
Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka.
Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga ya bayyana harin a matsayin “wani mummunan karya dokokin kasa da kasa, wanda ke tababtar da cewa Rasha ba ta mutunta rayukan fararen hula da nauyin da ya rataya a wuyanta na kasa da kasa.”
Kawo yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ko Rasha ko Amurka ba su ce uffan kan lamarin ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link