An rantsar da Randrianirina shugaban Madagascar
[ad_1]
An rantsar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin Madagascar, bayan ya jagoranci hamɓarar da shugaba Andry Rajoelina.
Sabon shugaban Madagascar kuma ya jaddada cewa hawan sa, ba juyin mulki ba ne, domin ya samu goyon bayan kotun tsarin mulkin ƙasar.
Bayan ya sha rantsuwar kama aiki Kanal Randrianirina ya ce abubuwan da zai fi bai wa fifiko sun haɗa da ruwan sha da abinci da kuma kafa gwamnati.
Tsohon shugaban Ƙasar Rajoelina wanda ’yan majalisar ƙasar suka tsige bayan tserewarsa waje a ƙarshen makon jiya, ya yi Allah wadai da juyin mulki kuma yaƙi amincewa da murabus duk da baya cikin ƙasar.
Rajoelina ya ce ya tsere daga ƙasar ne saboda dalilai na tsaro, yayin da babbar kotun Madagascar tuni ta tabbatar da sahihancin sabon shugabancin na soji, sa’o’i ƙalilan bayan juyin mulkin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link