Sojoji da ministoci sun taya ni murnar cin zabe —Issa Tchiroma

[ad_1]



Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari cewa ministoci da manyan hafsoshin sojin ƙasar sun taya shi murnar bayan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala.

Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ministoci da manyan jami’an tsaron da ministocin sun kira shi a waya suna jaddada goyon bayansu da niyyar biyayya ga kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma abin da al’umma suka zaɓa.

Ya bayyana haka ne wani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana mai nuna godiya ga waɗanda suka goyi bayansa, tare da jaddada cewa wannan lokaci yana da muhimmanci matuka ga kasa.

Ya ce, “Ina godiya daga zuciyata ga ministoci da jami’an gwamnati da suka kira ni kwanan nan domin nuna goyon bayansu. Wannan ba lokaci ba ne na wasa ko lissafi — lokacin ne da makomar ƙasa da zaman lafiya ke cikin haɗari, kowa sai ya zaɓi bangarensa, kuma da dama sun riga sun yi hakan,” in ji shi.

Bakary ya ƙara da cewa wasu manyan hafsoshin soji sun tabbatar masa da cewa suna tare da al’umma, ba tare da la’akari da matsayi ko iko ba.

“Ina godiya ga wasu manyan hafsoshin soji da suka bayyana cewa ba za su ci amanar aikinsu na kare al’umma ba. Ina fatan sauran za su bi sahu nan gaba, domin tarihi zai tuna da waɗanda suka zaɓi al’umma fiye da jin daɗin kansu.”

Ya kuma yi kira ga ’yan jarida da su guji yaɗa labaran karya ko na son zuciya.

“’Yan jarida, kada ku bari a mayar da ku kayan aikin yaɗa labaran da ba su da tushe saboda neman matsayi ko abin duniya. Matasa na kallon ku a matsayin abin koyi — kada ku zama abokan gaba ga al’umma.”

A ƙarshe, Bakary ya yi kira da a haɗa kai da a zauna cikin shiri da kwarin gwiwa.

“Lokaci yana da tsanani, amma  kyakkyawan fata ya fi ƙarfi. Mu tashi tsaye, mu haɗa kai, mu kasance cikin shiri. Makomar ƙasar nan tana hannunmu.”

Sai dai har yanzu hukumar zabe ta Kamaru ba ta fitar da sakamakon zaɓen ba.

Ana sa ran nan da ranar 26 ga watan nan da muke ciki hukumar za ta sanar da sakamakon zaɓen da aka gudanar a ƙarshe makon da ya gabata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *