Kwankwaso Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jos, Ya Nemi Hukumomi Su Ɗauki Mataki
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da harin Jos, inda ya yi kira da tsaurara tsaro a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa, Kwankwaso ya ce harin da aka kai wa al’ummar Gari Ya Waye a Jihar Filato, wanda ya yi ajalin mutane 27 tare da jikkata wasu da dama, abin takaici ne.
- Ghana Ta Sallami Kocinta Kafin Fara Gasar Kofin Duniya
- Sauya Sheƙar Gawuna Zuwa ADC Babban Koma Baya Ne Ga APC – Bashir Ahmad
Ya danganta yawaitar irin wannan tashin hankali da gazawar shugabanci, yana mai cewa dole ne a ɗauki lamarin da muhimmanci.
Ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da zaman lafiya ga kowa, ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.
Haka kuma, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma al’ummar yankin.
A nasa ɓangaren, gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya tabbatar da cewa mutane 28 ne suka mutu a yayin harin.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da alƙawarin cewa za a kamo waɗanda suka aikata laifin.
Hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike domin gano maharan, inda ‘yansanda da sauran jami’an tsaro ke sintiri a dazukan da ke kusa da yankin, tare da ƙara tsaurara tsaro domin hana sake faruwar irin wannan hari.